✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 3 sun mutu, 21 sun jikkata a turmutsitsin karɓar kuɗin tallafi a Borno

An tabbatar da mutuwar mutum uku tare da jikkatar wasu da dama sakamakon turmutsutsu a yayin wani taron rabon kuɗaɗen tallafi a garin Bama da…

An tabbatar da mutuwar mutum uku tare da jikkatar wasu da dama sakamakon turmutsutsu a yayin wani taron rabon kuɗaɗen tallafi a garin Bama da ke jihar Borno.

Wasu bayanai sun bayyana cewa ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya da UNICEF suka shirya rabon tallafin.

Shaidun gani da ido sun ce, turmutsitsin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 8:00 na safe a makarantar firamare ta Kasugula, daya daga cikin cibiyoyin bayar da tallafi da aka kebe a garin Bama.

Rahoton na nuni da cewar waɗanda suka ci gajiyar shirin sun taru ne domin karɓar tallafin kuɗi na naira 28,500 kowannensu.

Turmutsitsin ya faru ne a daidai lokacin da jama’a suka yi cincirundo a bakin  kofar makarantar, lamarin da ya haifar da turereniya.

 

Wani dan shekara 60 mazaunin Mazaɓar Bukar Tela, wanda lamarin ya ritsa da shi ya rasu ne a lokacin da aka isa babban asibitin garin Bama. Daga baya wasu mutane biyu da suka jikkata sun mutu yayin da ake jinya a asibiti.

Majiyar ta ce, waɗanda suka samu raunukan sun hada da mata da maza, kuma an tura karin sojoji wurin da lamarin ya faru domin dawo da zaman lafiya tare da saukaka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.

Daga bisani aka bayar da gawarwakin mamatan ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kungiyar ta ICRC_Africa ta ce ba ta da hannu a aikin rarraba kudaden a Bama wanda ya haifar da wannan turmutsitsin da ya kai ga asarar rayuka, kamar yadda aka gabatar a cikin rahoton farko.