Sojojin Nijar sun na da Janar Abdourahmane Tchiani a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya bayan sun yi wa Shugaba Bazoum juyin mulki.
Janar Abdourahmane Tchiani shi ne Kwamandan Rundunar Tsaron Shugaban Kasa, wadda ta kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, mai shekaru 64 a ranar Laraba.
- Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta soke lasisin Kannywood
- Ministoci: Dalilin da Tinubu bai ba da suna daga Kano ba
- Juyin mulki: Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukan agaji a Nijar
Sanarwar da rundunar sojin ta yi a ranar Juma’a ta tabbatar da kifar da gwamnatin Bazoum, tare da ayyana Janar Tchiani a matsayin “Shugaban Majalisar Mulkin Sojin Kasa,” sannan ya gabatar da jawabin tabbatar karbe mulki daga farar hula.
Wane ne Abdourahmane Tchiani?
Janar Abdourahmane Tchiani shi ne kwamandan rundunar tsaron shugaban kasar Nijar, mukamin da ya rike tun daga sheakrar 2015.
Tchiani, mai shekaru 62 dan asalin Tillaberi ne da ke Yammacin kasar, yankin da yawancin sojojin kasar suka fito.
Amini ne ga tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou – wanda ya mika wa Bazoum mulki a shekarar 2021 — ya zama kwamandan rundunar tsaron shugaban kasa.
Shi ne kuma ya jagoranci murkushe wani yunkurin juiyn mulki a kasar a shekarar 2021, wanda sojoji suka yi gabanin rantsar da Bazoum a matsayin shugaban kasa kuma magajin Mahamadou Issoufou.
Shi ne kuma jagoran juyin mulki na biyar a kasar da aka yi ranar 26 ga watan Yuli, 2023, na uku a yankin Sahel cikin shekaru uku, wanda kuma ya girgiza yankin da ma duniya.
MDD ta dakatar da ayyukan agaji a Nijar
Juyin mulkin da suka yi wa Bazoum dai na shan Allah-wadai daga kasashen duniya suna masu kira ga sojojin da su gaggauta sako Bazoum.
Sojojin sun sanar da nadin Janar Abdourahmane Tchiani ne jim kada bayan Majalisar Dinkin Duniya ta sanar cewa ta dakatar da ayyukanta na jin kai a kasar ta Jamhuriyar Nijar.
Majalisar dai ta bayyana cewa mutum sama da miliyan hudu ne suke tsananin bukatar agaji a matalauciyar kasar.
Da yake sanar da juyin mulkin ta talabijin a ranar Laraba, kakakin sojojin, Kanar Manjo Amadou Abdramane, ya ce sun yi hakan ne domin kawo karshen matsalar rashin tsaro da durkushewar tattalin arziki da kuma rashin shugabanci na gari a kasar.
Nan take ya sanar hana zirga-zarga daga karfe 10 na dare suz 7 na safe da kuma rufe iyakokin kasar tare da jingine kundin tsarin mulkin kasar da ma sauke daukacin masu rike da mukaman siyasa da dangoginsu a hukumomi da cibiyoyin gwamnati. Haka kuma ya kuma bukaci kasashen waje da su guji tsoma baki, yana mai tabbatar da cewa za su kare lafiyar Mista Bazoum.
Bazoum ya yi turjiya
Sai dai daga bisani Bazoum ya fitar da sanarwa cewa nasarar da kasar ta samu na tabbatar da tsarin dimokuradiyya zai samu kariya.
Shi kuma ministan harkokin wajensa, Hassoumi Massoudou, ya ayyana kansa a matsayin shugaban gwamnati, ya kuma sanar cewa shugaban kasan yana cikin koshin lafiya a hannun sojojin da ke tsare da shi.
Yadda TChiani ya yi wa Bazoum juyin mulki
Juyin mulkin ya faro ne bayan an wayi garin Talata da ganin dakarun rundunar da Janar Tchiani yake jagoranta sun tsare daukacin hanyoyin shiga da fita fadar shugaban kasar da ke birnin Yamai.
Duk da hakan ba su dauki wani matakin soji a sauran wurare ba, duk da cewa sun hana shiga ko fita daga fadar shugaban, inda suka tsare Mista Bazoum.
Bayan tsawon lokaci, jama’ar kasar suka yi zargin yunkurin juyin mulki ne magoya bayan shugaban suka yi zanga-zangar neman sojojin su sako shi zuwa fadar shugaban kasar, amma sojojojin suka tarwatsa su.
Daga bisani a cikin dare sojojin suka sanar da yi masa juyin mulki, kuma tun daga lokacin yana tsare a hannunsu.
A safiyar Juma’a dai ministan harkokin wajen Faransa ya sanar cewa shugaban kasarsa, Emmanuel Macron, ya tattauna da Bazoum, wanda ya ce ana iya magana da shi kuma yana cikin koshin lafiya.
Goyon bayan juyin mulki
A ranar ce kuma kasar ta haramta kowane irin zanga-zanga, bayan wasu magoya bayan juyin mulkin sun kai hari tare da kone-kone a hedikwatar jam’iyyar Bazoum ta PNDS Tarayya.
Sanarwar da ma’aikatar harokin cikin gidan kasar ta fitar ta umarci jami’an tsaro da su kare dukiyar kasar tare da cewa gwamnati za ta ladabtar da duk wanda ya saba sabuwar dokar domin ba za ta lamunci lalata dukiyar kasa ba.
Juyin mulki na 4 a Nijar
Kasar Nijar dai wannan shi ne juyin mulki na hudu da aka yi tun bayan samun ‘yancin kanta a 1960. A lokuta da dama kuma an sha yin yunkurin kifar da gwamnati a kasar ba tare da nasara ba.
Wannan kuma shi ne karo na hudu a cikin shekaru uku da suka gabata da sojoji suka yi juyin mulki a yankin a Nahiyar Afirka.