✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta soke lasisin Kannywood

Gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin masana’antar Kannywood da gidajen Gala. Shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano, Malam Abba El-Mustapha ne ya…

Gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin masana’antar Kannywood da gidajen Gala.

Shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano, Malam Abba El-Mustapha ne ya sanar da haka da safiyar Juma’a.

El-Mustapha ya ce hakan na nufin babu wanda zai ci gaba da yin fim a jihar Kano sai ya sabunta rajista da hukumar.

Abba El-Mustapha ya zama shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano

Wakar Cin Zarafi: ’Yan Kannywood sun caccaki Davido

Wannan soke lasisin ya shafi masu fitowa a fim, da masu shiryawa, da kasuwancinsa.

Su kuma gidajen rawar Gala an dakatar da su nan take har sai an tantance su.