Hedikwatar Tsaron Nijeriya DHQ ta ce sojojin ƙasar sun yi nasarar kashe ’yan ta’adda 254 da kuma kama 264 a cikin mako guda a faɗin ƙasar.
Daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron Manjo Janar Edward Buba ne ya tabbatar da hakan a wani taron manema labarai a ranar Juma’a.
Ya bayyana cewa a samamen da jami’an tsaron suka kai a faɗin ƙasar, sun ceto mutum 73 waɗanda aka yi garkuwa da su.
A yankin Arewa maso Gabas, Buba ya ce dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP 63, sun kama 13 tare da ƙwato bindigogin AK-47 guda 47 sauran tarin makamai da alburusai.
A yankin Arewa ta tsakiya, ya ce dakarun Operation Safe Haven da Whirl Stroke sun kashe ’yan ta’adda 35, sun kama wasu 72 tare da kubutar da wasu mutane biyar da aka yi garkuwa da su a jihohin Binuwai, Filato da Taraba a cikin mako guda.
A yankin Arewa maso Yamma kuma, Buba ya ce dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe ’yan ta’adda 128, sun kama 27 tare da kubutar da mutane 65 da aka yi garkuwa da su a yayin arangama daban-daban a jihohin Katsina, Zamfara da Sakkwato.
Buba ya ce, dakarun Operation Whirl Punch sun kama wasu mutane 42 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne da kuma masu tayar da kayar baya a wani wurin haƙar ma’adinai da ke yankin Kwali a Abuja.
Ya ce sojojin sun kuma kashe ‘yan ta’adda 14 tare da kama wasu 54 a yankunan Jihar Kaduna da Abuja.
A yankin Neja-Delta, Buba ya ce dakarun Operation Delta Safe sun gano tare da lalata haramtattaun matatun man fetur 67, jiragen ruwa 70, tankunan ajiya 125 da motoci 12.
A yankin Kudu maso Kudancin Nijeriya, sojojin sun samu nasarar ƙwato gangar mai 20,643 daga hannun ɓarayin mai wanda kuɗin man ya kai kimanin naira biliyan 2.6.
Sojojin sun ce duk a cikin mako guda, sun yi nasarar ƙwato makamai 5,083 daga hannun ’yan ta’addan da kuma tsabar kuɗi naira 748,430.
Sauran abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da motoci 18 da babura 40 da wayoyin hannu 74 da ɗimbin harsasai da bindigogi.