✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Gwamnan Kaduna ya koma APC

PDP ta ce sauya shekar da tsohon gwamnan ya yi ba za ta shafi farin jinin jam’iyyar ba a zabe mai zuwa.

Watanni biyar bayan barin tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya koma Jam’iyyar APC.

Tsohon gwamnan, wanda ya yi mulkin jihar daga 2012 zuwa 2015 a karkashin Jam’iyyar PDP, da ya sha kaye a hannun tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai a zaben 2015 a jihar.

Da yake tsokaci kan lamarin, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya ce, “Tun daga ranar da muka sanar da sauya sheka daga Jam’iyyar PDP, jam’iyyun siyasa da dama suke ta tuntubar mu ciki har da Jam’iyyar APC mai mulki.

Mun haɗu muka tattauna tun ranar da muka bar tsohuwar jam’iyyarmu. Don haka, tun daga ranar 12 ga Fabrairu, 2024, ni da wakilan sauran ‘yan siyasa mun yanke shawarar komawa Jam’iyyar APC.

Bayan mun yanke shawarar ne muka gana da gwamnan jihar muka tattauna da shi. Muka ce masa mun yarda mu shiga jam’iyyar ne bisa gayyatar da muka samu.

Tsohon gwamnan ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su bi shi a jam’iyya mai mulki domin su ba da gudunmawarsu wajen ciyar da jihar da kasa gaba.

Da yake mayar da martani game da shigar tsohon gwamnan cikin Jam’iyyar APC, Sakataren Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna, Malam Ibrahim Wosono ya ce, matakin da Yero ya ɗauka bai zo da mamaki ba.

A cewar Wosono, arzikin jam’iyyarsu ba ya hannun kowa, don haka zuwansa Jam’iyyar APC mai mulki ba zai shafi arzikin jam’iyyar a zabe mai zuwa ba.

“Yana da ‘yancin sauya sheka daga kowace jam’iyya zuwa wata jam’iyya, amma idan zai iya tunawa ya taba zama kwamishina a karkashin Jam’iyyar PDP, ya taba zama mataimakin gwamna a PDP, sannan kuma ya yi gwamna a karkashin jam’iyyar PDP.

“APC da ya koma yanzu ita ce jam’iyyar da ta kayar da shi a zaben 2015, kuma APC ce ta kai shi kotu har ma da gidan yari,” in ji shi.

A cewarsa, APC guda ce ta kai shi [Yero] EFCC, kuma har yanzu shari’ar tana ci gaba da gudana.

Dangane da ko zuwansa Jam’iyyar APC ba zai shafi PDP ta kowace fuska ba, Wosono ya ce, “A matsayinsa na tsohon gwamna, yana da mabiyansa, amma zan ce arzikin Jam’iyyar PDP ba ya dogara ga hannun wani.

“Idan za a iya tunawa PDP na da tarihi, Obasanjo ya bar PDP, Atiku ya taba ficewa daga PDP, gwamnoni da dama sun bar PDP, jam’iyyar kuma tana nan a raye.

“Don haka sauya shekar Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, ba na jin za ta shafi farin jinin Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa da yardar Allah,” in ji Wosono.