✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin al’adun kabilar Kare-Kare ke kawo zaman lafiya

Bikin na bana ya kayatar matuƙa duk da matsanancin matsalar tattalin arziki da ake fama da shi.

Bikin al’adar kabilar Kare-kare da ake kira da bikin “Bala Barama” wasu kuma na kiran sa da bikin wasan “Makwi” bikin ne da ake yi duk shekara.

Mahalarta biki sukan taru a garin Jalam da ke Karamar Hukumar Dambam a Jihar Bauchi da nufin sada zumunci da murnar kammala girbin amfanin gona da shirin fara farauta.

Garin Jalam wurin da ake yin bikin tsohon gari ne, akwai ganuwa guda 12 a garin, kuma daga cikin wadannan ganuwa guda hudu suna taka muhimmiyar rawa wajen shirya wannan biki.

Wadannan ganuwa hudu su ne “Dala Indi, Gawai, Dala Gamari da kuma Fi’ili”

Daya daga cikin dattawan garin Jalam kuma Sa’in Jalam Alhaji Ahmad Aliyu Jalam ya bayyana manufar yin wannan biki wato “Bala Barama.”

Ya ce ma’anar Bala ita ce Sakawa ma’anar Bara kuma Farauta, saboda haka wannan bikin saka farauta ne.

Shi wannan biki ba wanda ya san lokacin da aka fara shi saboda al’ada ce ta mutane kuma kullum suna tafiya ne da kayansu.

Sain Jalam ya ce, “Kuma bikin sau daya ake yi duk shekara, kuma duk wani bakakaren da yake Taraba da kasar Kamaru da Nijar da Adamawa duk inda suke za su zo wannan biki.

“Sannan Karamar Hukuma na zuwa karbar haraji a lokacin bikin.”

Ya kara da cewa, “Kasancewa al’ada ce ba a rasa camfi da tsafi a ciki, amma a yanzu an cire tsafi da camfin, saboda shi Makwi wato shugaban al’adar kabilar kare da muke da shi a baya wanda ya rasu kusan shekara 15 zuwa 20 suka gabata ya fito fili ya ce, shi Musulmi ne ba ya so ya mutu yana tsafi.

Ya ce, duk abin da yake na tsafi ne a cire a cikin bikin wanda kuma halal ne a ci gaba.

Sai aka zauna da malamai aka cire duk wani abu da yake ciki na tsafi da camfi.

Kuma a jawaban Makwi zai nuna muhimmancin zumunci da illar gulma da bakar magana a kan aure a daina, kuma ya ce duk wani mai yi wa wani hassada da tsegumi to zai kifa shuri a kansa, manufar in ya kifa shurin to mai yin mummunar abu ba zai samu wani alheri ba a shekarar baki daya.

Haka kuma zamani ya yi tasiri domin da in aka yanke fili da za a yi wasan ba wanda ya isa ya gifta ta cikin filin, amma yau ba haka ba ne, amma a yanzu filin ma da ake wasan bai kai yadda ake yin sa a da ba.”

Sain Jalam ya ce, ba za su bari a daina wannan al’ada ba, ‘‘duk yanayin da muka shiga ba za mu bari a yi watsi da wannan biki na al’ada ba.

“Muna kokari mu koyar da ’ya’yannmu muhimmancin riko da al’adunsu, kuma duk da harshen Hausa ya yi tasiri a tsakaninmu, ba ya cinye al’ada, harshen kawai yake tabawa.”

Bikin na bana ya kayatar matuka, inda ya samu halartar dubban ’yan kabilar duk da matsanancin matsalar tattalin arziki da ake fama da shi, da suka taru don tattauna matsalolin da suke damun al’ummarsu.

A lokacin bikin na bana an ga matasa dauke da kwari da baka da fatanya da sanduna wanda ke nuna cewa su mafarauta ne, kuma manoma ne, sannan matasansu sun fito sun yi fareti sun yi rawa kuma sun yi taken Nijeriya da yaren Kare-Kare, haka kuma mata sun yi wasanninsu daban-daban.

Da yake jawabi a wajen bikin, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa Alhaji Mohammed Auwal Jatau ya ce, gwamnatinsa ta himmatu wajen inganta ilimi da al’adu da wayar da kan jama’a.

Ya tabbatar wa al’ummar Jihar Bauchi cewa, za su ci gaba da bayar da goyon baya da inganta shagulgulan al’adu a jihar baki daya.

A jawabin godiya, shugaban kwamitin riko na Karamar Hukumar Dambam, Ahmed Mohamed Danbam ya nuna godiya ga Gwamna Bala Mohammed bisa yawan ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar a Karamar Hukumar.

A nasa jawabin Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Bauchi, Alhaji Ahmed Aliyu ya gode wa Gwamnan Jihar Bauchi saboda gagarumin gudummawar da ya bayar ta kudi da duk abin da ake bukata saboda samun nasarar bikin.

Shi ma Makwi Usmanu Sabo ya hori jama’a da su kula da zumunci, su rike noma da nema ba tare da wasa ba.