✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutun Ƙaramar Sallah

Ministan ya buƙaci Musulmai da su yi riƙo da halayen da suka koya a watan Ramadan.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata da Laraba mai zuwa a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan Sallah karama.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya ranar Lahadi a Abuja.

Tunji-ojo, cikin saƙon taya murna da babbar sakatariyar ma’aikatar, Aishetu Gogo Ndayako ta fitar, ya taya al’ummar Musulmin Najeriya murnar kammala azumin watan Ramadan na wannan shekarar.

Ministan, ya buƙaci Musulmi da su yi koyi da kyawawan halaye, kyautatawa, soyayya, hakuri, zaman lafiya da kuma tausayi kamar yadda manzon Allah S.A.W, ya koyar.

Tunji-ojo, ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu haɗin kai domin ɗorewar zaman lafiya a ƙasar nan.

A cewar sanarwar, “Ministan ya yi wa ɗaukacin al’ummar Musulmi barka da Sallah tare da addu’ar Allah ya ƙaro zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.”

Ana sa ran za a yi sallah a ranar Talata ko Labara da zarar an ga watan Shawwal na shekarar 1445 bayan hijira.