✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nijeriya ta soke ba da tallafin karatu a ƙetare

Hukumar Bunƙasa Arewa maso Yamma NWDC ta soke bayar da tallafin karatu.

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da tsarin bai wa ɗalibai tallafi domin samun damar zuwa ƙetare ƙarin ilimi.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, shi ne ya sanar da wannan mataki, da ke nufin cewa za a kawo ƙarshen wannan tsari da aka share tsawon shekaru ana aiwatarwa.

Mista Alausa ya bayyana cewa wannan matakai ya samu ne sakamako nazari da aka yi wajen sanya ƙaƙƙarfan jari a manyan makarantun ƙasar.

Ministan ya ce daga yanzu babu batun bai wa ’yan ƙasar kuɗaɗen ƙaro ilimi daga ƙetare, saboda yanayi da ake ciki da ma kyawun tsari da ake da shi a cikin ƙasar.

A cewarsa, dukkannin kwasa-kwasan da ’yan Nijeriyar ke zuwa wasu ƙasashen domin nazarin su, akwai su a cikin jami’o’i da ma kwalejojin fasaha masu nagarta da ake da su.

Ministan ya ce kuɗaɗen da ake kashewa wajen daukar nauyin karatun ɗaliban a ƙetare, zai fi dacewa a sanya su wajen inganta jami’o’in da kwalejojin da ake da su.

Sanarwar na zuwa ne a yayin da Hukumar Bunƙasa Arewa maso Yamma NWDC ta soke bayar da tallafin karatu ga ɗaliban da suka fito daga yankin.

Makonni kaɗan da suka gabata ne Hukumar ta NWDC ta fitar da sanarwar cewa tana neman haziƙan ɗalibai da suka fito daga yankin domin ɗaukar nauyin karatunsu a wasu ƙasashe ƙetare.

Sai dai wata sanarwa da hukumar ta fitar safiyar wannan Juma’ar, ta ce an soke tsarin, inda za ta mayar da hankali kan wasu ababen domin bunƙasa yankin.