Gwamnatin Nijeriya ta ayyana gobe Alhamis 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar albarkacin bikin murnar Ranar Ma’aikata ta Duniya.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a yammacin wannan Larabar.
- AU ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Gabon
- Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu
Sanarwar ta ambato ministan yana yaba wa ma’aikatan ƙasar kan sadaukarwa da jajircewar da suke yi wajen gudanar da ayyukansu.
Ministan ya kuma yaba musu kan gudunmawar da suke bayarwa wajen ciyar da Nijeriya gaba.
Ana dai gudanar da bikin Ranar Ma’aikata a ranar 1 ga watan Mayun kowace shekara a sassan duniya.