Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a, 18, da kuma Litinin, 21 ga watan Afrilun 2025 a matsayin ranakun hutun bikin Easter a faɗin ƙasar.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
- Barcelona da PSG sun tsallaka zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai
- DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo
A jawabin da Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida , Dokta Magdalene Ajani ta fitar, Ministan ya nemi mabiya addinin Kirista su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ƙasar addu’o’in zaman lafiya da haɗin kai.
Yayin da yake taya mabiya addinin Kirista murnar wannan lokaci, Mista Tunji yana kuma kira ga al’ummar Nijeriya da su haɗa hannu da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a ƙoƙarin da take yi na inganta rayuwar al’umma ta hanyar ci gaban ƙasa.