✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ACF ta nemi Gwamnatin Tarayya ta kawo ƙarshen kisan jama’a a Filato

Ƙungiyar ta ce dole ne a haɗa kai domin kawo ƙarshen zubar da jinin jama'a a jihar.

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa wajen kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato.

Ƙungiyar ta bayyana baƙin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da ƙananan yara.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Farfesa T.A. Muhammad-Baba ya fitar, ACF ta yi tir da waɗannan hare-hare tare da miƙa sakon ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma ɗaukacin jama’ar Jihar Filato.

Ƙungiyar ta ce hare-haren na ƙara jefa yankin Arewa cikin mawuyacin hali na rashin tsaro.

ACF ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci a wuraren da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga tare da haɗa kai da al’ummomin yankin domin daƙile barazanar tsaro.

Haka kuma, ƙungiyar ta nemi gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri da kuma kama waɗanda ke da hannu a ta’asar.

Ƙungiyar ta jaddada buƙatar wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato tare da buƙatar a haɗa kai da shugabannin gargajiya, dattawa, ƙungiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki domin daƙile lamarin.

ACF ta kuma bukaci al’umma su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanai kan duk wani abu da ka iya kawo matsala.