✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro ta sake dawowa a Bauchi

Muna zargin wani bako da ya zo daga Zamfara da wasu tsirarun ’yan sanda da ’yan banga.

Kasar Hakimin Lame da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi yanki na cikin yankuna mafiya girma da tarin jama’a a karamar hukumar da jihar.

Yankin ya yi iyaka da jihohin Kaduna da Filato da Kano da Yobe, da kuma dajin Lame- Burra da Falgore.

A kwanakin baya matsalar tsaro ta yi kamari a yankin har ta jawo wasu mutane suka fara kaura zuwa cikin garin Bauchi da wasu garuruwa.

Aminiya ta ruwaito yadda Hakimin Lame, Sarkin Yakin Bauchi, Alhaji Aliyu Yakubu Lame ya hada hannu da maharba da jami’an tsaro da taimakom Gwamnan Jihar Bauchi da Karamar Hukumar Toro wajen shiga cikin dajin da kauyuka inda suka kori ’yan ta’addar.

Sai dai a makon jiya, ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutum uku ciki har da wata mace tare da kashe Sarkin Ririwai, Alhaji Garba Badamasi bayan sun sace shi daga fadarsa a Gundumar Lame da ke Karamar Hukumar Toro.

Hakimin Alhaji Aliyu Yakubu Lame ya tabbatar da faruwar hakan lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan lamarin, inda ya ce abin takaici ne yadda ayyukan ’yan bindigar ke kokarin damowa a yankinsa.

Sarkin Yakin ya ce, masu garkuwa da mutanen da farko sun yi garkuwa da mutum uku ciki har da wata matar aure, kafin su je su dauki sarkin a fadarsa, bayan sun yi masa duka, ya samu raunuka da dama a kan hanyarsu ta zuwa maboyarsu, wanda aka ce sakamakon raunin da ya samu ne ya kasa tafiya, sai suka kashe shi, suka jefar da gawarsa.

Sarkin Yakin ya ce, kwana biyu kafin su je gidan sarkin, sun je gidan wani matashi don su sace shi, suka kasa karya kofarsa, sai suka fasa masa katanga kafin su iya shiga, suka dauki matarsa, aka aika musu da Naira miliyan hudu, suka amsa, sannan suka rike wanda ya je kai kudin.

Sarkin Yakin ya ce, suna zargin wani bako da ya zo daga Zamfara da wasu tsirarun ’yan sanda da ’yan banga da hannu cikin wannan lamari.

Ya yi kira ga Gwamnan Jihar da Mai martaba Sarkin Bauchi da Shugaban Karamar Hukumar Toro su taimaka a sake tsarin tsaro a yankin.

Ya ce, suna godiya ga Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed saboda taimakon da yake bayarwa kan tsaro kuma suna rokon kudin da ake bayarwa kada ya rika tsayawa a karamar hukuma kawai, ya rika isa har kasashen hakimai da gundumomi don a rika tallafa wa kungiyoyin sa-kai da ke kula da yankunan.

Mutanen garin Ririwai sun ce, a ranar Juma’a 15 ga Maris, 2024, wasu ’yan bindiga sun kai hari kauyen, inda suka tafi kai-tsaye zuwa fadar Sarkin Ririwai, suka tafi da shi wurin da ba a bayyana ba.

Sun ce, suna cikin tunanin makomar sarkinsu ne aka samu labarin sun kashe shi, sun jefar da gawarsa.

Har zuwa lokacin rubuta wannan labari, Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ba ta ce uffan kan lamarin ba, domin Kakakinta SP Ahmed Mohammed Wakili bai amsa kiran waya ba kuma bai amsa sakon waya da na WhatsApp da aka aika zuwa lambar wayarsa ba.