✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya ƙaddamar da jirage 2, ya buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro

Shugaban ya ce ci gaban ƙasa ya dogara ne ga zaman lafiya da tsaro.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci sojojin Najeriya su ƙara jajircewa wajen yaƙar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan.

Ya ce zaman lafiya, dimokuraɗiyya, da ci gaban tattalin arziƙi duk suna dogara ne da tsaron ƙasa.

Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin wani bikin ƙaddamar da sabbin jiragen sama guda biyu ƙirar Agusta 109 Trekker a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Bikin ya kasance wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 61 da kafuwar Rundunar Sojin Saman Najeriya.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne, ya wakilci Tinubu a wajen bikin.

Ya ce Najeriya na buƙatar ingantaccen tsaro domin ’yan ƙasa su samu damar yin harkokin rayuwa cikin kwanciyar hankali.

“Dimokuraɗiyya da tattalin arziƙin Najeriya na buƙatar cikakken tsaro. Dole ne a murƙushe waɗanda ke barazana ga zaman lafiya.

’Sojoji masu ƙarfi da kayan aiki masu inganci na da muhimmanci ga makomar ƙasar nan,” in ji Tinubu.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sabunta kayan aikin soji tare da saka hannun jari a fannin tsaro don tunkarar barazanar ‘yan ta’adda da sauran matsalolin tsaro.

“Wannan ci gaban zai taimaka wajen jawo saka hannun jarin a cikin gida da waje, sannan ya samar da cikakken tsaro a ƙasa,” in ji shi.

Ya kuma buƙaci rundunar soji da ta kasance a shirye don samar da zaman lafiya.

A nasa jawabin, Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Hasan Abubakar, ya bayyana cewa sabbin jiragen suna da amfani matuƙa ga harkokin soji da na jin-ƙai.

Ya ƙara da cewa, tuni aka karɓi sabbin jirage tara tun daga shekarar 2024, kuma ana sa ran samun wasu 49 cikin shekaru biyu masu zuwa, ciki har da jiragen yaƙi na zamani da na ɗaukar kaya.

Abubakar, ya bayyana cewa an riga an horar da matuƙa jirage takwas da injiniyoyi 18 don aiki da sabbin jiragen, yayin da wasu ke ci gaba da karatu a ƙasashen waje.

Tinubu, ya buƙaci rundunar sojin sama da ta kula da sabbin jiragen da ƙwarewa domin amfanin ƙasa.