✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Kasar Nijar ya haramta wa ministoci karin aure

Shugaba Bazoum ya bukaci duk ministan da ke son kara aure ya sauka da mukaminsa

Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum, ya haramta wa ministocinsa karin aure.

Bazoum ya ce duk ministan da ke son yin karin aure to ya sauka daga kujerarsa,  a wani mataki da shugaban ya ce zai taimaka wajen a rage yawan haihuwa barkatai a kasar.

“Na shaida wa ministocina cewa na haramta musu karin aure, matukar suna cikin gwamnatina.

“Idan akwai ministan da ke son ya yi karin aure ba za mu hana shi ba, amma kuma wajibi ne ya sauka dama mukamin Gwamnatin Tarayya,” inji shi.

Ya sanar gargadin ne a wurin wani taron mata da aka gudanar a ranar 13 ga watan Mayu, a kasar, inda mahalarta suka yi ta sowa suna yabo.

Sai dai kalaman nasa sun haifar da ce-ce-ku a Jamhuriyar Nijar, inda wani bangare yake ta caccakar shi a kan matakin da ya dauka na hana kara aure.

A lokacin da yake jawabin, shugaban kasar ya ce yawan al’ummar Jamhuriyar na ta karuwa, ta yadda hakan ke barazana ga jin dadin al’ummar kasar, bunkasar masana’antu da kuma rayuwar yau da kullum.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda ya ce maza ke dora wa mata nauyi, tare da bukatar daukar mataki kan irin halin da ke jefa su a cikin al’umma.