✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta zartar wa wanda ya kai wa ’yan sanda hari hukuncin kisa

An zartar wa wani mutum hukuncin kisa a kasar Saudiyya ranar Talata saboda kai wa wani dan sanda hari tare da ba da mafaka ga…

An zartar wa wani mutum hukuncin kisa a kasar Saudiyya ranar Talata saboda kai wa wani ’yan sanda hari.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce an yanke wa Anwar bin Jaafar bin Mahdi al-Alawi hukuncin kisa ne bayan samun sa da laifin bude wa wani ofishin ’yan sanda wuta.

Haka kuma an same shi da laifin baar da mafaka ga wani wanda jami’an saro ke nema kan mallakar makami ba bisa ka’ida ba.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta fitar ta kara da cewa kisa shi ne hukuncin duk wanda aka samu da irin wannan laifi.

(SPA).