✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fasto ya yi wa mataimakiyarsa fyade

Babban limami ya yi mata fyade a lokacin da take tsaka da sauraron wa'azi

Wata mataimakiyar fasto mai shekara 23 ta maka faston da take matsayin na’ibarsa a kotu, inda take zargin shi da yi mata fyade sau biyu.

Mataimakiyar faston ta bayyana wa kotun yadda limamin nata, mai suna Bishop Daniel Oluwafeyiropo, ya yi mata fyade ne a lokacin da take tsaka da kallon wa’azi a talabijin a gidansa da ke unguwar Lekki a watam Yunin shekarar 2020.

An  gurfanar da Bishop Daniel, wanda shi ne ya assasa cocin Reign Christian Ministry yake kuma jagorantatrsa, ne bisa tuhumar sa da aikata fyade da cin zarfi ta hanyar lalata, amma ya musanta zargin.

Mataimakiyar faston da aka sakaya sunanta, ta bayyana cewa a shekara 2018 ta fara sanin limamin cocin.

Ta ce sa fara sanin sa ne a lokacin da kawarta ta gayyace ta domin yin abada a cocin da ke yankin Akoko a Jihar Ondo, kafin daga baya ta koma mabiyar cocin, har ta samu daukaka zuwa mataimakiyar fasto.