✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yakin Sudan: Akwai yiwuwar maniyyata su kara biyan wasu kudin 

Sai dai hukumar ba ta bayyana ko matakin na nufin, maniyyata aikin hajji ne za su biya ƙarin kuɗin ba

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta tabbatar da cewa yaƙin da ake yi a kasar Sudan zai shafi jigilar maniyyatan Najeriya na bana, wanda ka iya sanadin karin kudin kujerar.

A ranar Talata hukumar da kamfanonin sufurin jiragen sama na cikin gida suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar jigilar mahajjatan ta bana.

A makon jiya dai sun gaza yin hakan saboda batun ƙarin kuɗi.

Sai dai hukumar ba ta bayyana ko matakin na nufin, maniyyata aikin hajji ne za su biya ƙarin kuɗin da dogon zagayen zuwa kasa mai tsarki ko a’a ba.

Kwamishinan Tsare-tsare da Gudanar da Gikin Hajji a hukumar, Abdullahi Magaji Hardawa, ya ce har zuwa yanzu ba a cimma matsaya kan ko mahajjata ne za su yi ƙarin kuɗin ba.

A cewarsa, matuƙar ba a buɗe sararin samaniyar kasar Sudan ba, har aka fara jigilar maniyyatan bana daga Najeriya, to dole sai jiragen sama sun yi zagaye, wanda zai haddasa ƙarin kuɗi.

Jami’in ya ce babban hatsari ne jirgin sama ya ratsa ta sararin samaniyar Sudan, shi ya sa hukumomin ƙasar suka dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a kasar.

Harɗawa ya ce matuƙar aka fara jigilar maniyyata aikin hajji na bana, ba tare da an bi ta Sudan ba, za a fuskanci matsaloli guda biyu ko fiye.

“Na farko, in ba za a shiga ta sararin samaniyar Sudan ba, dole za a shiga ta wasu ƙasashe. To ƙasashen nan akasari, za a biya su kuɗin ratsawa ta sararin samaniyarsu.

“To maimakon kuɗin da za a biya na ƙasa ɗaya, wato Sudan. (A yanzu) mai yiwuwa a biya na ƙasashe da yawa. Kun ga an samu ƙarin kuɗaɗe ke nan,” in ji shi.

Na biyu, a cewarsa, tun da akwai ƙarin tazara kamar na sa’a biyu a tafiyar jirgin sama, man da jirgin yake sha ma zai ƙaru, wanda ke nufin ƙarin kuɗin jigilar alhazai.

Abdullahi Harɗawa ya ce kamfanonin jiragen sama sun sa hannu a kan yarjejeniyar jigilar aikin hajjin na bana ne bayan an daddale tsakaninsu da Hukumar NAHCON a kan matsalolin da za a iya fuskanta.

Ya ce: “Sun amince sun sa hannu ɗin, amma an yarda akwai bukatar a san yadda za a yi, a ƙara musu farashi.”

Jami’in ya ce kasanceaw maniyyata sun riga sun biya kuɗi, “bisa yadda aka tallatar masa,”  yanzu ba zai iya tabbatar da ko za a bukaci maniyyaci ya kara biyan wasu kudin ba.

“Amma dai abin da nake tabbatar muku so hi ne, akwai bukatar ƙarin kuɗi. Akwai tazara da yawa. Akwai ɗawainiya da yawa. Karin kuɗin nan daga ina zai fito? Shi ne ba a cimma matsaya ba”.

Kamfanonin sufurin jiragen saman da suka sa hannu kan yarjejeniyar sun haɗar da – Air Peace da Azman Air Services da Aero Contractor da kuma Max Air.