Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta ƙaddamar da bincike dangane da zargin almundahana kan Shugaban Gidan Talabijin na jihar (ARTV), Alhaji Mustapha Adamu Indabawa.
Binciken na zuwa bayan ƙorafin da Ƙungiyar ’Yan Jarida (NUJ) da Ƙungiyar Ma’aikatan Gidajen Rediyo da Talabijin (RATTAWU) suka gabatar wa Gwamna Abba Kabir Yusuf.
- ‘Mun tura wa EFCC $760,000 kuɗin makaranta da Yahaya Bello ya biya wa ’ya’yansa’
- Na gamsu da yadda jama’a suka fito zaɓe — Gwamna Inuwa
Ƙungiyoyin na zargin Alhaji Indabawa da almundahanar kuɗin da suka kai Naira miliyan ɗari da kuma saɓa ka’idar aiki.
Ana iya tuna cewa Alhaji Indabawa na ɗaya daga cikin shugabannin hukumomi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa a watannin baya bayan nan.
Bayanai sun ce masu binciken sun titsiye Alhaji Indabawa a ranar Juma’ar da ta gabata kan zargin sama da-faɗin fiye da Naira miliyan 60 da kuma zargin satar tsabar kuɗi har Naira miliyan uku na Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) da ya yi ikirarin an sace a cikin motarsa.
Duk laifukan da ake zargin Alhaji Indabawa sun ci karo da sashe na 26 na Kundin Dokokin hukumar PCACC kuma mafi ƙanƙantar hukuncin shi ne cin sarƙa ta shekara uku.
A yayin da Aminiya ta tuntubi Alhaji Indabawa dangane da taƙaddamar, ya ce ba shi da ta cewa tunda har lamarin yana gaban hukuma.