✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na fi karfin kujerar Ministan Abuja a Gwamnatin Tinubu

El-Rufai ya ce idan ya sauka da kujerar gwamnan Kaduna ba zai kara komawa ba

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce ba zai karba ba, ko an nada Ministan Babban Tarayya ba a Gwamnatin Bola Tinubu da za a rantsar ranar 29 ga wata Mayu da muke ciki.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a yayin da ake shirye-shiryen rabon mukamai a sabuwar gwamnatani, inda ake hasashen za a nada shi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ko kuma ministan Abuja.

“Ko an ba ni ministan Abuja ba zan karba ba. Na sha fada cewa ba na maimaita aji, kuma na san akwai matasan suka fi dacewa da kujerar,” in ji shi.

Da yake jawabi a wurin taron kaddamar da wani littafi a Abuja ranar Talata, ya bayyana cewa, “Ba zan koma gidan jiya ba. Kai! Tun da na bar Abuja ban sake komawa ba sai a 2016 da aka nada abokin karatuna a matsayin minista, ya bukaci gani na.

“Yanzu na tsufa da fita yin rusau, gara a samo matasa masu jini a jika.”

Ya ci gaba da cewa, “Nan da kwana 19 zan bar Kaduna, kuma ba zan kara zuwa ba sai idan ya zama dole. Ni ba na ma na ma tunanin kujerar ministan Abuja. Na gama da ita kuma ba zan ce komai kan ayyukan wadanda suka yi bayana ba.

El-Rufai, ya ce, wanda ke cikin mutanen da suka yi tsayuwar daka wajen ganin mulki ya koma yankin Arewa bayan wa’adin Shugaba Buhari — wanda hakan ya kai Tinubu ga nasara — ya ce ya fi karfin kujerar ministan.

A zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, gwamnan ya kasance ministan Abuja, inda ake ganin ya yi rawar gani wajen zamantar da birnin da kuma samar da cigaba.