✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta aike da jiragen kayan tallafi zuwa Afghanistan

Saudiyya ta aike da jirage shida makare da kayan tallafin don rage matsananci hali da mutanen Afghanistan ke ciki.

Kasar Saudiyya ta aike da manyan jirage dauke da kayan agaji zuwa kasar Afghanistan sakamakon halin matsi na yunwa da dubban mutanen kasar ke fuskanta.

Tallafin na zuwa ne karkashin gidauniyar Sarki Salman (KSRelief), wadda ta aike da samanda tan 65 na kayan tallafi da kuma kwandunan kayan abinci sama da 1,647, kamar yadda Kamfanin Dillacin Labaran Saudiyya (SPA) ya bayyana a ranar Alhamis.

Shugaban gidauniyar, Abdullah al-Rabeeah, ya ce an aike da jirage shida kasar dauke da kaya.

Ya kara da cewa Saudiyya za ta sake aika tirela 200 daga Pakistan zuwa Afghanistan don rage matsananci hali da mutanen kasar ke ciki.

Kungiyar Kasashen Larabawa, a taron da ta gudanar a ranar Talata a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, ta amince da a tallafa wa Afghanistan.

Sama da mutum miliyan 38 ne a Afghanistan ke fama da karancin abinci, wanda hakan ya jefa rayuwar da dama cikin wani hali, wasu kuma ya tilasta musu yi kaura zuwa wasu kasashe da ke makwabtaka da Afghanistan.

A baya lokacin da Taliban ta yi mulki daga 1996 zuwa 2001, ta kafa dokoki masu tsauri tare da hukunci mai tsanani ga duk wanda ya karya dokokin.

A wannan karon ma, bayan sake kafa mulki, Taliban ta sake kafa wasu dokoki wadanda mutane da dama daga ciki da wajen kasar ke ganin sun yi tsauri da yawa.

Taliban ta hana mata zuwa makaranta ko wurin aiki da kuma fitowa a shirye-shiryen gidajen talabijin.