Kungiyar Al’ummar Arewa (CNG) ta yi wa Jihar Katsina tsine domin zanga-zangar sai-baba-ta-gani kan garkuwa da aka yi da daliban Makarantar Sakandaren GSSS Kankara.
A safiyar Alhamis ne dandazon ’yan kungiyar ke fara macin gangamin da aka yi wa taken #BringBackOurBoys; daga nan za su isa Daura, mahaifar Shugaban Kasa Buhari, inda yake hutu.
- Abin da ya sa na tube Sanusi daga Sarautar Kano —Ganduje
- Gwamnati ta bude iyakokin Najeriya guda hudu
- An gano inda daliban Makarantar Kankara suke —Masari
“Babu tunani ga duk dan Arewan da zai zauna yana kallo an bar ’yan bindiga da ’yan ina-da-kisa da masu garkuwa da mutane na abin da suka ga dama a Arewa, duk da muhimmancin yankin a kasa,” inji kungiyar.
A ranar da Buhari ya sauka a Daura ne aka yi garkuwa da daruruwan daliban GSSS Kankara, a Jihar Katsina mai fama da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Mun kawo rahoton yadda wasu ’yan daba suka tarwatsa taron da CNG ta shirya a Kaduna ranar Litinin, kan matsalar tsaro da ke addabar Arewa da ma Najeriya.
Kakakin kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman ya ce harin ba zai hana ta yin kira da a sako daliban “da sauri, a raye kuma ba da lahani ba.”
Suleiman ya ce CNG na sane cewa an jibge ’yan sanda a Jihar Katsina, don haka ya yi kira da a guji hana halastacciyar zanga-zangar da ya ce za ta gudana cikin lumana.