Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya yi wa fursunoni 39 a gidajenn yari daban-daban da ke jihar afuwa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa al’ummar jihar a Litinin, a wani bangare na bikin ranar Sabuwar Shekara.
- EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar jin-kai kan badakalar 37bn
- Muhimman abubuwa daga jawabin Tinubu na Sabuwar Shekara
Ya bayyana cewa an yi wa fursunonin afuwa ne don ba su damar komawa mutanen kirki.
“A cikin sabuwar shekara, kuma bisa shawarar da Majalisar Jiha ta bayar, na ba da izinin yi wa fursunoni 39 afuwa.
“Daga cikin su akwai fursunoni 26 aka sake su nan take, sai ragowar 13 ’ya sisi-kwandem da sassauta hukuncin da aka yanke musu.
“Fatan wadanda suka ci gajiyar za su sauya su rungumi rayuwa mai kyau su zama mutanen kirki.”
Gwamnan, yayin da yake yi wa jama’ar jihar fatan samun wadata a shekarar 2024, ya bukace su da su ci gaba da amfani da darusan da suka koya masu kyau a 2023.
“A 2024, za mu mayar da hankali kan gina Gombe, ba za mu bar kowa a baya ba, kamar yadda aka bayyana a cikin kasafin kudinmu na 2024.”