✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimman abubuwa daga jawabin Tinubu na Sabuwar Shekara

Sabon mafi karancin albashin ma'akata na tafe in ji Shugaba Tinubu

Ga wasu muhimman abubuwa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fada a jawabinsa na Sabuwar Shekarar 2024 ga al’ummar Najeriya.

Wanna shi ne jawabinsa na sabuwar shekara na farko, wata bakwai da hawansa kan karagar mulki.

  1. Za mu yi aiki tukuru domin tabbatar da ganin duk dan Najeriya ya amfana da wannan gwamnatin. Har marasa karfi duk babu wanda za a bari a baya.
  2. A karkashin hakan za mu gabatar da sabon tsarin albashi mafi karanci ga ma’aikata a cikin wannan Shekaran.
  3. Ba zan daga kafa ga duk wanda na bai wa mukami ba, idan bai yi aiki yadda ya dace ba.
  4. A 2024 za mu kara hobbasa wajen soma tace danyen mai a Matatar Mai ta Fatakwal da ta Dangote wadanda za su soma aiki gadan-gadan
  5. Mun shirya domin farfado da duk fannoni, bayan hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasa da muka samar cikin watanni bakwai na 2023..
  6. Domin tabbatar da samar da abinci da tsaro, za mu gaggauta noma hekta 500,000 na masara da shinkafa da alkama da dawa da sauran hatsi.
  7. Duk da cewa ba za mu iya bugun kirji cewa mun shawo kan duk matsalolin tsaro ba, amma muna aiki tukuru domin samar da zaman lafiya a gidajenmu da wuraren aiki da lungu da sako.
  8. .Gwamnatinmu ta fahimci cewa babu wani cigaba da za a samu muddin wutar lantarki ba ta wadata ba.
  9. Muna shirin kaddamar da wasu ayyukan shimfida layukan samar da wutar lantarki da kuma inganta tashoshin samar da wutar a fadin kasar nan
  10. Ni da Shugaban Gwamnatin Jamus, Olaf Schlz muka kulla yarjejeniyar yin aiki cikin gaggawa domin kammala aikin da kamfanin Siemens ke yi, wanda zai samar da wutar lantarki ga gidaje da wuraren kasuwanci wanda aka soma a 2018.
  11. A 2024 za mu yi hobbasa wajen ganin duk wasu batutuwa na kudi da haraji da suka kamata a sanya su bisa tsari, an yi su yadda ya dace saboda kada a samu koma baya.
  12. Zan soke duk abun da zai kawo tarnaki ga kasuwanci a kasar, ko zai hana Najeriya zama cibiyar kasuwanci ga masu son zuba jari na cikin gida da na kasashen waje.
  13. A duk wata tafiya da nayi zuwa kasashen waje, sakon da nake bayarwa shi ne Najeriya a shirye take domin yin kasuwanci da kowa.
  14. Mun kaddamar da noman rani a filin da ya kai hekta 120,000 a Jihar Jigawa a watan Nuwamban 2023, a karkashin shirinmu na bunkasa noman alkama.