✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar jin-kai kan badakalar 37bn

Ana zargin tsohuwar ministar da hada baki da wani mutum wajen yin sama da fadi da kudaden.

Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), ta gayyaci tsohuwar ministar jin-kai, Sadiya Umar Farouk, kan zargin ta da karkatar da sama da Naira biliyan 37.

EFCC ta bukaci Sadiya ta bayyana a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Laraba mai zuwa don yin cikakken bayani game da yadda kudaden suka yi batan dabo.

Sadiya Faruk na cikin ministocin Buhari da aka rika zargin su da cin hanci a lokacin da suke kan karagar mulki, duk da dai ta sha musanta zarge-zargen da ake yi mata.

EFCC ta zargi Sadiya da hada kai da wani mai suna James Okwete wajen wawure wadannan kudi, sai dai tuni tsohuwar ministar ta ce ko sunan mutumin ba ta taba ji ba.

Bayanai na nuna cewa James ya shafe kusan kwanaki 10 a hannun jami’an EFCC, suna masa tambayoyi.

Daga Sadiya zuwa masu ba ta shawara da mataimakanta kan harkokin yada labarai babu wanda ya yi wa manema labarai karin haske kan wannan dambarwa.

Sai dai a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a makon jiya, Sadiya ta ce ba ta taba sanin wani mai suna James Okwete ba, ballantana ta yi wata hulda da shi.

A baya-bayan nan dai an sha yin kira kan a binciki tsofaffin wadanda jami’an gwamnatin Buhari.