Akalla mutane 50, cikinsu har da kananan yara 8 sun rasa rayukansu, a dalilin nau’ikan iftila’i daban daban masu alaka da mamakon ruwan saman da ya shafe makwanni biyu yana sauka a wasu yankunan Pakistan, lamarin da haifar da ambaliyar ruwa.
Wani jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa a Pakistan din, ya ce baya ga gomman rayukan mutanen da suka salwanta, wasu akalla 87 sun jikkata.
- Bidiyon Dala: Ganduje ya yi martani kan sammacin hukumar yaki da rashawa
- Bunkasa Kasuwanci: Dokoki 4 da Tinubu ya rattaba wa hannu
RFI ya ruwaito cewa wannan lamari dai na zuwa bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya rika sauka tun daga ranar 25 ga watan Yuni zuwa yanzu a wasu yankunan gabashi da arewa maso yammacin kasar.
Akasarin asarar rayukan da aka samu a lardin Punjab ne a dalilin jan wutar lantarki da kuma ruftawar gine-gine kan mutane.
A yankin Shangala na lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke Arewa maso Yammacin kasar ta Pakistan, jami’an ceto sun samu nasarar ciro gawarwakin yara 8 da shekarunsu suka kama daga 12 zuwa 15 bayan zaftarewar kasar da ya binne su, yayin da suke ci gaba da laluben ragowar da ba a gani ba.