✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bunkasa Kasuwanci: Dokoki 4 da Tinubu ya rattaba wa hannu

Akwai dakatar da harajin kashi 5% na ayyukan sadarwa da kuma harajin fitar da kayayyaki na cikin gida.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan wasu dokoki hudu a kokarinsa na farfado da tattalin arzikin Najeriya kamar yadda gwamnatinsa ta kudirta.

Shugaban ya dauki wannan muhimmin mataki na bai wa ‘yan Najeriya fifiko da kuma magance manufofin kasafin kudi da ba su dace da kasuwanci ba.

Dele Alake, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru wanda ya bayyana haka ga manema labarai ya fada ranar Alhamis cewa, shugaban ya sanya hannu kan dokokin

Daga ciki akwai dakatar da harajin kashi 5% na ayyukan sadarwa da kuma harajin fitar da kayayyaki na cikin gida.

Shugaba Tinubu har ila yau, ya sa hannu a kan Dokar Kudi ta 2023, wadda a yanzu ta jingine fara aiki da sauye-sauyen da ke cikin dokar daga ranar 23 ga Mayun 2023 zuwa 1 ga Satumban 2023, hakan zai yi daidai da mafi karancin kwanaki 90.

Shugaba Tinubu ya kuma rattaba hannu a kan dokar karbar harajin shigo da kaya da aka yi wa garambawul ta 2023, wanda a yanzu za ta fara aiki daga 27 ga watan Maris zuwa 1 ga Agustan 2023.

Tinubu ya kuma bayar da umarnin dakatar da wani sabon haraji mai suna Green Tax da aka bullo da shi kan robobin da ake amfani da su da wani nau’in haraji da ake karba a kan wasu motoci da ake shigowa da su kasar.

Shugaba Tinubu ya kuma rattaba hannu kan dokar garambawul na kudin harajin kwastam, 2023, inda ya sauya ranar fara canjin haraji daga ranar 27 ga Maris, 2023, zuwa 1 ga Agusta, 2023.

Alake ya nanata matsayar shugaban kasar, inda ya bayyana cewa gwamnati ta amince da masu kasuwanci, na gida da na waje, a matsayin muhimman abubuwan da ke haifar da karuwar GDP da samar da ayyukan yi.

Gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da tsare-tsare masu kyau da kuma samar da abubuwan kara kuzari don samar da yanayi mai kyau na kasuwanci don bunkasa a cikin kasar.

Alake ya bayyana ce wa, Shugaba Bola Tinubu na fatan tabbatar wa ‘yan Najeriya da suka damka masa amanar mulki cewa, ba za a sake samun wani nauyi na haraji ko ka’idojin kasuwanci da ke hana ci gaban tattalin arziki ba.

Gwamnati ta ci gaba da sadaukar da kai don magance korafe-korafe da samar da yanayin da zai inganta ci gaban kasuwanci, samar da ayyukan yi, da ci gaban tattalin arziki gaba daya.