Shugaba Bola Tinubu ya ce damuwarsa a yanzu ba ta zargin gwamnatocin da suka gabata ba ce, illa ɓullo da tsare-tsaren da suka dace domin ciyar da Najeriya gaba.
Tinubu ya kuma ce yanzu haka ya fi maida hankali wajen ɗaukar matakan da suka dace domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar, samar da tsaro, da kuma sauran matsalolin da ke dulmiyar da ita.
Jawabin shugaba Tinubun na zuwa ne bayan wasu mukarraban gwamnatinsa sun zargi gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da laifin gurgunta tattalin arzikin kasar.
Ana iya tuna cewa, a bikin magance ƙarancin abinci da aka gudanar a Minna, babban birnin jihar Neja, da dama daga cikin mukarraban Tinubu ciki har da Ministan Kuɗi Wale Edun, suka ɗora laifin matsalolin tattalin arziki da kuma tsaro kacokan kan Gwamnatin Buhari.
Sai dai Tinubun ya ce ba halinsa ba ne ya ɗora wa gwamnatocin da suka shuɗe laifi kan taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma rashin tsaro tsaro da Najeriya ke fama da shi.