✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon Dala: Ganduje ya yi martani kan sammacin hukumar yaki da rashawa

A yanzu Muhuyi Rimin Gado ba zai iya yi wa Ganduje adalci ba saboda ta yiwu a akwai gilli a zuciyar sa.

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da martani dangane da sammacin da hukumar yaki da rashawa da kula da korafin jama’a ta jihar ta ce ta aika masa.

Aminiya ta ruwaito cewa hukumar PCACC mai yaki da rashawa da kula da korafin jama’a ta Kano ta nemi Ganduje ya bayyana a gabanta domin ba da bahasi kan bidiyon da ake zargi ya nuna yana karbar cin hancin daloli.

A hirarsa da kafar talabinjin ta Channels a ranar Alhamis, shugaban hukumar yaki da rashawar ta Kano Barrister Muhuyi Magaji ya ce ya rattaba hannu akan wata takardar sammaci da aka aika wa tsohon gwamna Ganduje.

A cewarsa, a cikin wasikar, hukumar ta bukaci tsohon gwamnan ya bayyana a gabanta a makon gobe domin bayar da bahasi a kan wannan faifan bidiyo na dala.

Wannan sammacin na zuwa ne bayan binciken da hukamar ta ce ta fara a kan lamarin, kasa da makonni uku da dawo da Barista Muhuyi Magaji akan kujerar shugabancin hukumar.

Ya ce gabanin haka, hukumar ta tabbatar da sahihancin faifan bidiyon, wanda a baya can ake tababa akan ingancinsa.

Sai dai tsohon gwamna Ganduje ta bakin Kwamishinansa na harkokin raya karkara da ci gaban al’umma, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya mayar da martani dangane da wannan sabon yunkuri na hukumar yaki da rashawar ta Kanon.

Ya bayyana cewa, “Tun shekaru biyu zuwa uku da suka gabata mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mika wannan batu a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kuma yanzu haka maganar tana kotu, don haka bai kamata a ce wani ya yi sammaci ya ce yana bincike akan lamarin dake gaban kotu”

A hannu guda kuma, kungiyoyin gwagwarmayar shugabanci na gari sun fara tofa albarkacin bakin su game da batun, inda Kwamared Ibrahim Garba Maryam, mamba a zauren gamayyar kungiyoyin na jihar Kano ya ce, “abinda ya kamata mutane su gane shi ne lokacin da wannan abu ya faru shi gwamna yana da kariyar doka, yanzu kuwa babu wannan kariya don haka dole yanzu doka ta yi aiki a kansa a yi bincike, amma idan za a yi bincike tilas ne a yi bisa adalci.

“Shi cin hanci da wanda ya bayar da wanda ya karba duk suna ciki, saboda haka ina wanda ya bayar din? Ina kamfanonin da suka yi aikin? Ya kamata a hada dasu.”

Baya ga kungiyoyin fararen hula, masu sharhi a fagen siyasa da harkokin yau da kullum a jihar ta Kano na ci gaba da bayyana fahimtar su a kan lamarin.

Alhaji Jafar Sani Bello daya daga cikin masu fashin baki akan siyasa da al’amuran yau da kullum a Najeriya ya ce “Ni a gani na Muhuyi ya saki damarsa ta bincikar gwamna Abdullahi Umar Ganduje domin kuwa al’amarin ya faru lokacin yana kujerar shugabancin hukumar Rashawa ta Kano, amma bai ce komai ba kuma daga bisani suka yi fada har gwamnan ya sauke shi daga kujerar. Don a yanzu ba zai iya yin adalci ba ga tsohon gwamnan saboda ta yiwu a akwai gilli a zuciyar sa.”

Tun a shekara ta 2018 ne aka fara ce-ce-ku-ce akan wannan fefen bidiyo wanda mawallafin jaridar kafar Intanet ta Daily Nigerian wato Jafar-Jafar ya fara kwarmatawa lokacin da ake tunkarar zaben 2019, koda yake batun ya lafa daga bisani, amma masu kula da lamura na ganin sake bude shafin maganar ba zai rasa nasaba da kammala wa’adin mulkin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba da kuma yadda siyasar Kanon ke ci gaba da daukar sabon salo.