Shugaban Amurka Joe Biden ya ce jiragen yaki da kasarsa ta jibge a kusa da Isra’ila gargadi ne ga Iran ta shiga taitayinta.
Biden, wanda ya ce ya kamata Iran “ta yi hattara” a rikicin Isra’ila da kungiyar Falasdinawa ta Hamas, ya bayyana harin Hamas kan Isra’ila a matsayin “tsantsar rashin imani”.
- ‘ASUU ba za ta bar shiga yajin aiki ba sai gwamnati ta yi abin da ya makata’
- An kama shi kan yunƙurin fyaɗe ga ’yar shekara 85
Shugaban wanda ya ce kasarsa za ta kara taimakonta ga Isra’ila da makamai duk da cewa tana taimaka wa Ukraine da makamai da horon soji domin yaki da Rasha.
Hamas ta sako uwa da ’ya’yanta
Bangaren soji na kungiyar Hamas, ya yi ikirarin sako wata mace da kananan yara biyu daga cikin mutanen da kungiyar ta yi garkuwa da su a Isra’ila.
Rundunar al-Qassam ta fitar da bidiyon mutanen wanda kafar yada labarai ta Al Jazeera ta nuna a ranar Laraba, wanda a ciki aka nuwa wasu mayaka suna tafiya bayan sun bar matar da yaran a kusa da wata katanga da ake kyautata zaton yana tsakanin Zirin Gaza da Isra’ila.
Kawo yanzu dai hukumomin Isra’ila ba su yi magana kan bidiyon ba, sannan ba a iya tantance lokacin da aka dauki bidiyon ba.
Masar ta gargadi Isra’ila kafin harin Hamas
Kungiyar mayakan Hezbollah ta kasar Lebanon da ke musayar wuta da Isra’ila a ranar Laraba ta soki Biden kan matakin, tare da cewa ya nuna gazawar Isra’ila kuma a shirya mayakan kungiyar suke da su gwabza da sojojin Isra’ila.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da Kwamitin Tsaron Majalisar Dokokin Amurka ta gano cewa sai da kasar Masar ta gargadi Isra’ila, kan yiwuwar harin kungiyar Hamas, kwanaki uku kafin farmakin.
Dan majalisa kuma mamba a kwamitin, Michael McCaul, ya sanar da haka ne bayan wata ganawar sirrin kwamitin, amma ya ce, “ba na son bayyana wasu abubu na sirri saboda dalilan tsaro.
- Rikicin Gaza: Netanyahu na neman tayar da Yakin Duniya na Uku
- Gaza: Sudais ya yi tir da harin Isra’ila kan Falasɗinawa
A halin yanzu Isra’ila na kokarin farfadowa da daukar fansa bayan hari mafi muni a shekaru 75 da kungiya Hamas ta kai mata, inda mayakan kungiyar 1,500 suka kutsa cikin Isra’ila bagatatan, suka hallaka mutum 1,200 suka jikkata 2,700, tare da garkuwa da wasu 150.
A kan haka ne yanzu Isra’ila ke luguden bama-bamai a matsayin martani a yankin Falasdinawa na Zirin Gaza a yakin zuwa yanzu ya yi ajalin mutum 3,700 da suka hada da sojoji da fararen hula daga bangarorin biyu.
Sarkin Ingila ya la’anci harin Hamas
Sarki Charles na Uku na Ingilda ya yi tir da harin ranar Asabar da kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta kai wa Isra’ila.
yana mai ba da umarnin a rika sanar da shi halin da ake ciki, sannan ya ce Fadar Buckingham za ta ci gaba da sanya wanda lamarin ya shafa cikin addu’a.
Kungiyoyin Larabawa sun yi wa Isra’ila taron dangi
A ranar ce kungoyiyin Falasdinawa a Hamas da Islamic Jihad da kuma Hezbollah suka yi wa Isra’ila ruwan rokoki a cigaba da yakin da ake tsakaninsu.
Rundunar Al-Quds, reshen sojin Islami Jihad ta ce ta yi luguden wuta kan biranen Isra’ila da suka hada da Tel Aviv, Ashdod da Ashkelon da ke da iyaka da Zirin Gaza a ranar Laraba.
Ita kuma rundunar Ezzedine Al-Qassam ta kungiar Hamas, ta nufi filin jirgi na Gurion ne da nata rokokin, ko da yake rundunar sojin Isra’ila ta ce ba a kai hari a filin jirgin ba.
Hezboll kuma ta kai nata harin ne a matsayin martani kan kisan mayakanta uku da Isra’ila ta yi.
Jiragen yakin Isra’ila sun mayar da martani, a yayin da sojojinta suke ci gaba da mamaye yankin Falasdinawa na Zirin Gaza a rikicin.
Isra’ila ta kashe ma’aikatan jinkai
A Larabar ce kuma jiragen Isra’ila suka kashe wasu jami’an lafiya uku a cikin motar daukar marasa lafiya ta kungiyar Red Crescent a yankin na Gaza, sai na hudunsu a wani hari na daban.
Jamus ta roki Qatar ta lallashi Hamas
Hakan na zuwa ne a yayin da Jamus ta roki kasar Qatar ta sanya baki wajen lallashin kungiyar Hamas ta sako mutane 150 da ta yi garkuwa da su a harin da ta kai wa Isra’ila ranar Asabar.
‘A ci gaba da jinkan Falasdinawa’
A gefe guda, kasar Norway ta bukaci masu ba da tallafi na duniya su ci gaba da taimkawa domin kai dauki da kayayyakin jinkai ga Falasdianwa da harin Isra’ila ya shafa.
Norway wadda ke jagorantar ayyukan jinkai a Falasdinu ta yi kiran ne bayan kasashen Austria, Denmark, Germany da Sweden, sun ce za su janye tallafinsu ga Falasdinawa saboda harin kungiyar Hamas na ranar Asabar.
Amma Ministan Harkokin wajen Norway, Anniken Huitfeldt ya bayyana cewa ragewa ko daina tallafawa zai haifar da mummunan yanayi; hasali ma babu hujjar da ke nuna tallafin da ke zuwa ta hannun Norway na amfanar Hamas ko kawayenta.
Ya bukaci a ci gaba da taimakawa ta hannun Bankin Duniya da Majalisar Dinkin Duniyaa da sauran hukumomin kasa da kasa, domin Falasdinawa da Isra’ila ke ci gaba da ruwan bama-bamai a kansu.