✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP Ta Buƙaci A Binciki Mutuwar Mutane A Turmutsutsun Gidan Wamakko

Wannan ba shi ne karo na farko da a aka samu mutuwar mutane wurin karɓar sadaka ba a ƙasar nan.

Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato ta buƙaci a tsaurara bincike kan dalilin mutuwar mutane tara da kuma jikkatar waɗansu da dama a gidan tsohon gwamnan jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata,  rahotanni sun bayyana cewa, mutane tara sun mutu a turmutsutsu, yayin da da dama suka jikkata wurin ƙoƙarin karɓar sadakar shirye-shiryen Sallah a gidan tsohon gwamnan.

Dubban mutane ne dai suka je gidan tsohon gwamnan a ranar Alhamis domin karɓar tallafin abin da za su yi amfani da shi a bikin karamar sallah da ke tafe.

An tabbatar da cewa taron mutane ne ya yi yawa har wasu tara daga cikin masu ƙoƙarin karɓar sadakar suka riga mu gidan gaskiya.

Daga cikin waɗanda suka mutu akwai wata jami’ar sa-kai da ke taimakawa Hukumar Sibil Defens.

An ce, Fatima Bala, jami’ar sa-kai a Hukumar NSCDC ta rasa ranta ne a kokarin ceton wani yaro.

Fatima Bala ta yi nasarar ceto yaron da aka danne, sai dai ita kuma ta gamu da ajalinta.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da a aka samu mutuwar mutane wurin karɓar sadaka ba a ƙasar nan.

A makon da ya gabata, an samu rahoton mutuwar mutane goma a Bauchi, kana a Jami’ar Jihar Nasarawa wasu ɗalibai sun ransu wurin karɓar tallafin gwamnatin jihar.