✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN ya sake korar ma’aikata 40

Adadin waɗanda aka sallama a karkashin jagorancin Gwamnan Bankin Olayemi Cardoso ya kai 67.

Babban Bankin Najeriya CBN ya sake sallamar wasu ma’aikata aƙalla 40 daga bakin aiki.

Galibin waɗanda sallamar ta shafa na aiki ne a sashin habaka harkokin kudi, a wani mataki na kawo sauye-sauyen da bankin ke yi.

Aminiya ta ruwaito cewa an raba wa ma’aikatan wasiƙun sallamar ne a yammacin ranar Juma’ar da ta gabata, lamarin da ya sanya aka samu karancin bayanan waɗanda abin ya shafa.

Sai dai wakilinmu ya ruwaito cewa akwai sunan Musa Zgabawa Bulus, mataimakin daraktar sashin kula da kadarorin amsar lamuni ga kanana da matsakaitan masana’antu.

An kuma ruwaito cewa akwai masu mukamin mukaddashin darakta da kuma mataimakan darakta 22 daga sashin habaka harkokin kuɗi na bankin da lamarin ya shafa, sannan ragowar 18 ɗin sun fito ne daga bangaren kiwon lafiya da kuma cinikayya.

Ana iya tuna cewa a kwanakin baya, akwai kimanin ma’aikatan bankin 27 da aka fara sallama daga bakin aiki, duk da cewa a yanzu haka wasu bayanai na cewar akwai wasu da za a sallama a cikin kwanaki masu zuwa.

Daga cikin mutanen da aka fara sallaman, akwai daraktoci 8 da mukaddashin daraktoci 10 da mataimakan daraktoci 5 sai wasu manyan manajoji 4.

Da wannan kora da CBN yayi a yanzu, adadin waɗanda aka sallama a karkashin jagorancin Gwamnan Bankin Olayemi Cardoso ya kai 67.

Sai dai duk ƙoƙarin da wakilinmu ya yi domin jin tabakin daraktar yada labarai ta bankin Hakama Sidi Ali abin ya ci tura.