✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nikki Haley ta janye daga neman tikitin takara bayan shan kaye a hannun Donald Trump

A cikin manyan abokan hamayyar Trump, Haley ce kaɗai ta rage a cikin masu neman tikitin takarar.

Nikki Haley ta janye daga yunƙurin da take yi na neman tikitin tsayawa takarar Shugaban Kasar Amurka a jam’iyyar Republican.

Wannan dai ya biyo bayan rashin nasarar da ta yi a jihohi 14 a zabubbukan fidda gwanin da suka gudana a ranar ‘Gagarumar Talata’ a hannun abokin hamayyarta Donald Trump.

Tsohuwar Gwamnar Jihar South Carolina, wacce ta taba zama Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya a karkashin gwamnatin Trump, ta gabatar hakan ne a yayin wani jawabi a kusa da gidanta na South Carolina da misalin karfe 10 na safiya agogon Amurka a yau Laraba.

Haley ta sha fama da jerin rashin nasara, wadda ta samo asali daga jihohin Iowa da New Hampshire da Nevada har ma da jiharta ta asali South Carolina.

A jiya Talata, bayan kammala kada kuri’u a jihohi 15 a zabubbukan fidda gwanin da aka yi wa laƙani da ‘Gagarumar Talata’ ko Super Tuesday a Turance.

Texas da California na daga cikin manyan nasarorin da Trump ya samu a kan Nikki Haley yayin da ya samu goyon bayan daligets a jihohin Kudu masu ra’ayin mazan jiya da kuma na masu sassaucin ra’ayi irin su Virginia, ɗaya daga cikin jihohin da aka yi hasashen Nikki tana da babbar dama kan abokin hamayyarta.

A baya can ta lashe zaben a jiha daya tilo, Washington DC, sannan ta samu wani kaso mai tsoka a Jihar Vermont da ke Arewa maso Gabashin Amurka.

Nikki Haley dai ita mace ta farko wacce ba farar fata ba da ta nemi tikitin takarar Shugaban Kasa karkashin jam’iyyar Republican.

A cikin manyan abokan hamayyar Trump, Haley ce kaɗai ta rage a takarar, don haka janyewarta na ba da tabbacin cewar Trump zai samu tikitin takarar jam’iyyarsa ta Republican.

Tsohon Gwamnan Jihar Florida, Ron DeSantis na daga cikin ’yan jam’iyyar Republican da suka janye wa Donald Trump takara tun gabanin zaɓen fidda-gwanin.