✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutane 7 ‘yan gida ɗaya da wasu 38 a Binuwai

Cikin waɗanda suka mutun akwai akalla manoma 12 da ba su ji ba ba su gani ba.

Aƙalla mutum bakwai ’yan gida ɗaya da wadansu 38 sun gamu da ajalinsu a kauyen Gbagir da ke Karamar Hukumar Ukum a Jihar Binuwai.

Mutanen sun rasa rayukansu ne sakamakon rikicin da ya barke tsakanin wadansu kungiyoyin ‘yan bindiga biyu da ke rigimar fifiko a tsakaninsu.

Mazauna yankin sun ce lamarin wanda ya faru a ranar Talatar da ta gabata ya sanya fargaba a cikin zukatansu.

Wandansu da abin ya faru a idonsu sun ce, akasarin wadanda suka mutu ana zargin ‘yan bindiga ne da batun neman kwatar iko ya haɗa su faɗa kuma aka gaza sasantawa.

Bayanai sun ce cikin waɗanda suka mutun akwai akalla manoma 12 da ba su ji ba ba su gani ba, sakamakon ba-ta-kashin da aka yi tsakanin bangarorin biyu na ‘yan bindiga.

Mazauna yankin da suka tsere daga gidajensu sun ce, mutane da dama sun samu raunuka, yayin da an nemi wasu an rasa har zuwa safiyar Laraba.

Wani basaraken gargajiya a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai a Makurdi cewa an fara samu tashin hankalin ne a safiyar ranar Talatar da ta gabata.

Ya ce, shugaban wata kungiyar ‘yan bindiga a Binuwai ne ya yi garkuwa da wani shugaban ‘yan bindiga daga Jihar Taraba da ake kira Alhaji Gana da ‘yan uwansa waɗanda suka shahara wajen yin fashi da garkuwa da mutane ‘yan asalin unguwar Chinkai sannan daga bisani aka kashe su.

Basaraken ya ce bayan sace waɗanda aka kashe ɗin, an biya kuɗin fansa Naira miliyan 100 ga waɗanda abin ya shafa sannan aka kara Naira miliyan 5.

A cewarsa, kisan waɗanda aka yi garkuwa da su din tun a karshen makon da ya gabata ne ya tayar da hankalin ‘yan kungiyar Alhaji Gana a Jihar Taraba.

Wata majiyar soji da ta tabbatar da faruwar lamarin a garin Ukum, ta ce an yi arangama ne tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga guda biyu.

Majiyar ta ce an gano gawarwakin mutane da dama amma ba ta bayyana adadinsu ba.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Binuwai, Emmanuel Adesina, ya shaida wa manema labarai a Makurdi cewa, an tura karin jami’an ‘yan sanda zuwa yankin, yana mai cewa kawo yanzu an gano gawarwaki biyar.