Amurka ta fara kwashe ‘yan kasarta tare da sanar shirin rufe ofishin jakadancinta da ke Jamhuriyar Nijar na wucin gadi sakamakon juyin mulkin kasar a makon jiya.
Birtaniya ta ce za ta kwashe wasu jami’an ofishin jakadancinta da ke birnin Yamai a yain da tuni wasu kasashen Turai suka fara kwashe ‘yan kasarsu bayan masu zanga-zangar kyamar Faransa sun kai wa ofishin jakandacinta hari a ranar Lahadi.
- An cafke malami kan cakuda mata da maza a sahun Sallah
- Tinubu ya nada mace minista daga Kano, Matawalle, Bagudu, Lalong sun samu shiga
Shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani dai ya gargadi kasashen waje game da “game da kowane irin shisshigi a harkokokin cikin gidan” kasarsa.
Gwamnatin sojin dai ta haramtaa zanga-zanga, amma ana hasashen ranar Alhamis magoya bayan juyin mulkin za su yi zanga-zanga domin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kan Nijar.
Faransa wadda tsohuwar uwar gijiyar Nijar ce ta roki sabuwar gwamnatin sojin ta kare ofishin jakadancinta, bayan harin da aka kai masa.
Hairn ne ya sa a ranar Lahadi ofishin ya fara kwashen Faransawa daga Nijar zuwa birnin Paris saboda fargabar abin da zai iya biyo baya.
Ministan Tsaron Faransa, Sébastien Lecornu, ya ce sun kwashe mutum 1,000 daga Nijar da suka hada da Farasnsawa da ‘yan wasu kasashen Turai.
Rahotanni daga biranen Maradi da Yamai babban birnin Nijar sun nuna komai na tafiya lafiya, amma sojoji na sintiri a kusa da fadar shugaban kasa da wasu ofisoshin jakadanci da ma’aikatu.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya ce ya samu ganawa da hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum a ranar Laraba, inda ya jaddada aniyar Amurka na ganin an dawo da zababbiyar gwamnati a Nijar.
Kakakin ma’aikatar, Matthew Miller ya bayyana cewa duk da kwashe ma’aikatan ofishin jakadancin kasarsa, ofishin da ke birnin Yamai zai ci gaba da aiki.
Kasashe sun juya wa sojojin Nijar baya
Amurka na daga cikin manyan kawayen Jamhuriyyar Nijar, masu taimaka mata ta fuskar ayyukan jin kai da kuma tsaro, tana barazanar janye tallafinta saboda juyin mulkin da sojojin suka yi.
Tuni dama Faransa da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar turai (EU) suka janye nasu tallafin ga kasar da ke yankin Sahel.
Kungiyyar ECOWAS mai rajin raya tattalin arzikin yammacin Afirka da ke da kasashe 15 a matsayin mambobi, ta kakaba wa gwamnatin sojin Nijar takunkumin karya tattalin arziki saboda juyin mulkin.
‘Ba za mu karaya ba’
A ranar Larabar manyan hafsoshin tsaron ECOWAS sun yi wata ganawa a Najeriya kan juyin mulkin na Nijar, inda suka duba yiwuwar daukar matakin soji, idan ya zama babu makawa.
Sai dai a jawabinsa ranar Laraba, Janar Tchiani, wanda ya kwace mulki a ranar 26 ga watan Yuli ya yi wati da daukacin takunkuman a matsayin makirci domin tayar da zaune tsaye a Nijar, wanda ba zai sa sojojin su karaya ba.