Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewar duk wanda ke shirin shiga jam’iyyar; ciki har da jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, shi ne zai kasance shugabansu.
Ganduje ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, inda ya ce shi ne mutum mafi girma a jam’iyyar APC.
Ya ce, “Idan kana magana ne a kan APC, to, mu ne shugabanninta. Ba a Karamar Hukuma ko jiha ba, a kasa baki daya.
“Idan kai dan Jam’iyyar APC ne shugabanninta kake bi. Haka yake ga shugabannin mazabu da na jiha.
“Idan ka shigo APC a yau, kai ma mai bin bayan shugabanninta ne. Yana da kyau a kula da wannan; yaron gida da bako duka suna karkashin maigida ne.”
Ganduje, da yake ganawa da magoya bayan jam’iyyar a jihar, ya ce kada su tsorata don wani zai shiga cikinta.
Ya kara da cewar, “Kada ka ji tsoro saboda wani zai zo gidanka neman wani abu. Da ka je gidansa neman abu, da ya zo gidanka neman abu, wanne ka fi so?
“Wanda yake da abin da zai bayar shi ake kokarin zuwa gidansa, wanda kuwa ba shi da abun bayarwa shi ne yake neman wajen shiga.
“Ku ba ni aron kunnenku zan ba ku wani labari! Mene ne aikin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa? Shin iya Kano ne kadai? Jihohi 36 da Abuja duk inda na je ni sarki ne, ni malami ne, ni modibbo ne kuma ni alanguburo ne. Don haka a nan gida muna kira ga NNPP da ta kwaso kayan marmarinta ta zo inda za a adana mata su a firinji kada su lalace.
“Muna kiran su, su dawo APC. Shin laifi ne yin hakan? Mutumin da ke da abin da zai bayar shi ake roko, mutumin da zai bayar da abu shi ne zai yi roko don haka muna so su duba. Shugabancin kasar nan a jam’iyyarsu ba abu ne mai yiwuwa ba. To, idan abu ne mai kyau muna kira a gare su.
“Kamar yadda na fada muku, ko kai wane ko mene ne mukaminka a jam’iyyarku ko da kuwa kai ne ‘Jagora’ [Kwankwaso] da zarar ka shigo APC kakanka yana nan!
Aminiya ta ruwaito Kwankwaso, wanda shi ne shugaban NNPP, magoya bayan Kwankwasiyya da wasu daga sassan kasar nan, na kiransa da suna ‘Jagora’.
Ganduje ya ziyarci Kano a karon farko, tun bayan zaben 2023 da APC ta yi rashin nasara a zaben gwamnan jihar.
Ganduje dai ya ziyarci jihar ne, inda yake ganawa da masu ruwa da tsaki na jami’yyar.
A lokacin taron, Ganduje ya bukaci gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da ya dawo jam’iyyar APC.
Sai dai gwamnan ya yi fatali da bukatar Ganduje, inda ya ce tsohon gwamnan bai biyo hanyar da ta dace na zawarcinsa ba.