✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyi 5 na samun saukin tsadar rayuwa a Najeriya

Shawarwari kan yadda za a samu sauki a wannan yanayi na tsadar rayuwa

Hauhafan farashin kayan masarufi a Najeriya ya jefa iyalai da dama cikin halin ni-’yasu.

Janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi shi ne babban dalilin tashin gwauron zabon abubuwa a kasar; ko da yake wani masannin tattalin arziki, A.G Mukhtar, ya bayyana cawa karin haraji da tashin farashin canjin Dala sun taimaka wajen hauhawan farashi a kasar.

A kan haka ne ya ba ba da wadannan shawarwari kan yadda za a samu sauki a wannan yanayi na tsadar rayuwa.

1- Takaita kashe kudi

Mukhtar ya ce akwai bukatar al’ummar Najeriya su rika lissafi su guji  yin saye-saye barkatai, da haka ne za a adana kudade, a kuma rage wai nauyi biyan abubuwan da aka saya.

2- Hakura da kayan alfarma

Masanin ya kuma jaddada muhimmanci a hakura da sayen kaya na alfarma, a koma amfani da wadanda za su maye gurbinsu.

He said, “Avoid spending on things that are frequently used especially if their prices skyrocket except if they are a necessity like payment of medical bills.”

3- Daina tafiye-tafiye barkatai

Kamata ya yi a halin da ke ciki a hakura da  tafiye-tafiye da ba na dole ba, kamar na yawon bude ido, gara a adana kudin da za a kashe domin wasu bukatu da ke iya tasowa.

4- Kara hanyoyin samun kudi

Samun wasu hanyoyin samun kudaden shiga banda albashi zai taimaka sosai.

5- Zuba jari

Su daure su rika sanya jari da kasuwanci mai riba, mai maimakon kashe kudadensu barkatai. Da haka ne za su rika samun wasu kudaden gudanar da harkokinsu na yau da kullum.