Majalisar wakilai ta nuna damuwarta kan matsalar karancin takardun kudi a bankunan kasuwanci a fadin kasar nan, inda ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya shawo kan lamarin.
Matsalar karancin takardun kudade na kawo cikas ga harkokin tattalin arziki da kuma kawo wa ’yan kasa wahala inda masu harkar POS ke tatsar su.
Wakilanmu sun ruwaito cewa ’yan Najeriya na kara fuskantar wahala wajen samun takardar kudi domin hada-hadar yau da kullum.
Lamarin ya fi tsanani a yankunan karkara, inda ake da karancin bankuna da sauran hanyoyin hada-hadar kudi. A garuruwa da birane kuma, masu sana’ar POS suna wuce gona da iri ta hanyar cajar kwastomomi fiye da ykima.
- Mai aikin shara ya mayar da N40m da ya tsinta a Kano
- Dawowar rikicin daba ta addabi Kanawa
- ’Yan sanda sun kama mutum 3 da jabun kuɗi N129bn a Kano
“Na biya N500 don in cire N10,000 a garejin Jabi,” in ji Jennifer Samuel, wata ma’aikaciyar gwamnati a Abuja.
“Ina bukatan tsabar kudi domin in biya kudin mota zuwa Mararaba saboda direbobin tasi ba sa karban tiransifa, amma bai dace in biya N500 ba don kawai in samu N10,000,” in ji ta.
Wani dan kasuwa mai suna Abdulmumini Ibrahim ya ce ya biya N800 a POS domin karbar N20,000.
“Gaskiya takaita amfani da tsabar kudi yana da kyau ga duk al’ummar da ke son bunkasa amma Najeriya ba ta kai lokacin yin hakan ba.
“Dole ne gwamnati ta saka hannun jari kan ababen more rayuwa domin shawo kan mutane su amince da sabon tsarin. A yanzu, ya kamata su samar da karin takardun kudi,” in ji shi.
A kan haka ne Majalisar Wakilai ta umarni CBN ya magance matsalar domin sama wa ’yan Najeriya sauki, daga wannan yanayi.
Kiran na zuwa ne a bayan umarnin da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ga CBN da bankunan kasuwanci na su gaggauta warware matsalar karancin kudi da kuma cajin mutane da masu POS ba bisa ka’ida ba.
A makon jiya ne CBN ya umurci bankuna da su ba da fifiko wajen bayar da takardun kudade ga kwastomomi a kan kanta da kuma ta injinan ATM.
Umarnin wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Disamba, 2024, wani bangare ne na kokarin da bankin na habaka samuwar takardun kudade da kuma magance matsalar karancinsu.
A wani kudiri da Hon. Uguru Emmanuel, ya gabatar majalisar ta bayyana illar karancin takardun kudaden ga tattalin arziki da zamantakewa, wanda ya sa ’yan Najeriya da dama ba su iya samun kudade ko da na bukatun yau da kullun.
Ya yi nuni da cewa, yayin da ci gaban tattalin arzikin ya dogara kan sayayya da zuba jarin kasuwanci, matsalar karancin kudin ta zama babban cikas ga wadannan ayyuka.
Dan majalisar ya bayyana cewa a watan Disamban 2022 CBN N500,000 ne CBN ya iyakance a matsayin tsabar kudin da daidaikum mutane za su cira a banki, kamafnoni kuma Naira miliyan biyar.
Sai dai ya lura cewa bankunan kasuwanci sun yi watsi da wannan tsari, inda sukan takaita fitar da tsabar kudi zuwa Naira 10,000 ko kadai.
Ya kuma bayyana damuwa gama da yadda ake samun gibi tsakanin bankunan kasuwanci da masu harkar POS, wadanda ake ganin ba su da iyaka wajen samun kudi, inda sukan caji masu cirar kudi a wurinsu fiye da kima.
Dan majalisar ya yi gargadin cewa idan har CBN bai dauki matakin gaggawa ba, lamarin na iya kara tabarbarewa, musamman ma ganin lokacin bukukuwan ya gabato, lamarin da zai sa ’yan kasuwa cikin mawuyacin hali na tattalin arziki.
A karshe, majalisar ta umurci kwamitin harkokin banki da ya binciki matsalar tare da bayar da rahoto cikin mako guda.
Majalisar ta umurci CBN da ta gaggauta magance matsalar, idan dai ba shi ne ya haddasa karancin kudi ba.
Wakilanmu sun ruwaito cewa ’yan Najeriya na kara fuskantar wahala wajen samun takardar kudi domin hada-hadar yau da kullum.