✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai ciyo bashin Naira tiriliyan 39 daga kasashen waje

Tinubu ya jaddada gaggawar buqatar wadannan kudade, yana mai nuni da tasirin cire tallafin mai da raguwar kudaden shiga na cikin gida.

Shuganan Kasa Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Wakilai takardar neman amincewarta domin ya ciyo bashin jimillar kudi Naira tiriliyan 39 daga kasasahen waje domin aiwatar da wasu ayyuka.

A wasiku ukun da ya aike wa majalisar, wadanda shugabanta, Abbas Tajudeen, ya karanta a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya nemi goyon bayan majalisa domin ciyo bashin daga kasashen waje a shekarar 2025–2026.

Ya ce rancen na 2025–2026, ya kunshi Dala biliyan 21.5 (kimanin Naira tiriliyan 34) da Yuro biliyan 2.2 (kimanin Naira tiriliyan 3.96) da Yen na Japan biliyan 15 (kimanin Naira biliyan 164.7) da kuma Yuro miliyan 65 (kimanin Naira biliyan 116.79) a matsayin tallafi.

Yana kuma neman cin bashin cikin gida ta hanyar bayar da takardun lamuni na Dala biliyan biyu, kimanin Naira tiriliyan 34.285, don biyan basussukan fanshon adashi gata da suka taru.

Tinubu ya nemi amincewa da bayar da takardun lamuni na Naira biliyan N757.98 a cikin gida domin biyan basussukan fansho da suka taru har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.

Shugaban kasan ya bayyana cewa an tsara neman bashin ne don tallafa wa muhimman ayyukan a fannonin ababen more rayuwa, noma, lafiya, ilimi, da tsaro a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.

Ya bayyana cewa bayar da takardun lamuni na Dala biliyan biyu ya yi daidai da Dokar Zartarwa ta Shugaban Kasa da nufin samar kuɗin domin farfado da darajar Naira da gudanar da muhimman ayyukan samar da ababen more rayuwa da samar da ayyukan yi.

Tinubu ya jaddada gaggawar buqatar wadannan kudade, yana mai nuni da tasirin cire tallafin mai da raguwar kudaden shiga na cikin gida.

Ya lura cewa hakan zai magance rashin bin tanade-tanaden Dokar Gyara Fansho a baya saboda matsalolin samun kuɗi, da nufin dawo da ƙwarin gwiwa a tsarin fansho da inganta jin daɗin tsofaffin ma’aikatan gwamnati.

Dukkan buƙatun guda uku an miƙa su ga Kwamitin Kula da Kuɗi na Majalisar don ɗaukar matakan majalisa na gaba.