More Podcasts
Fara sana’a na cikin manyan jerin kalubalen da ’ƴan Najeriya suke fuskanta sakamakon wasu dalilai wadanda suka hada da rashin ilimi, ko Rashin wanda zai ba su shawara ko kuma, uwa uba, rashin jari.
Wasu bayanai da Hukumar Ƙididdiga Ta Kasa – NBS – ta fitar sun nuna cewa fiye da kashi 40 cikin 100 na matasan Najeriya suna sha’awar fara sana’a, amma sun kasa saboda rashin jari.
Haka kuma, wani bincike da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gudanar ya nuna cewa kashi 65 cikin 100 na matasa masu so su fara kasuwanci suna fuskantar babbar tangarda wajen samun jari daga bankuna ko hukumomin gwamnati.
Shin ko akwai wata hanya da matasa za su bi su fara sana’a ko da ba su da jari?
- NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Suka Fara Bacewa Yayin Bukukuwan Sallah
- DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah
Wannan shine batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan