Hauhafan farashin kayan masarufi a Najeriya ya jefa iyalai da dama cikin halin ni-’yasu.
Janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi shi ne babban dalilin tashin gwauron zabon abubuwa a kasar; ko da yake wani masannin tattalin arziki, A.G Mukhtar, ya bayyana cawa karin haraji da tashin farashin canjin Dala sun taimaka wajen hauhawan farashi a kasar.
A kan haka ne ya ba ba da wadannan shawarwari kan yadda za a samu sauki a wannan yanayi na tsadar rayuwa.
- An yanke mazakutar malamin allo daf da aurensa a Zariya
- An kama matar da ta sayar da kananan yara 42
1- Takaita kashe kudi
Mukhtar ya ce akwai bukatar al’ummar Najeriya su rika lissafi su guji yin saye-saye barkatai, da haka ne za a adana kudade, a kuma rage wai nauyi biyan abubuwan da aka saya.
2- Hakura da kayan alfarma
Masanin ya kuma jaddada muhimmanci a hakura da sayen kaya na alfarma, a koma amfani da wadanda za su maye gurbinsu.
He said, “Avoid spending on things that are frequently used especially if their prices skyrocket except if they are a necessity like payment of medical bills.”
3- Daina tafiye-tafiye barkatai
Kamata ya yi a halin da ke ciki a hakura da tafiye-tafiye da ba na dole ba, kamar na yawon bude ido, gara a adana kudin da za a kashe domin wasu bukatu da ke iya tasowa.
4- Kara hanyoyin samun kudi
Samun wasu hanyoyin samun kudaden shiga banda albashi zai taimaka sosai.
5- Zuba jari
Su daure su rika sanya jari da kasuwanci mai riba, mai maimakon kashe kudadensu barkatai. Da haka ne za su rika samun wasu kudaden gudanar da harkokinsu na yau da kullum.