Wasu mawaƙan jam’iyyar APC da ke Jihar Jigawa, sun bayyana ɓacin ransu kan yadda gwamnatin jihar ta yi watsi da su, duk da irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023.
Mawaƙan wajen su 35, sun gudanar da wani taro, inda suka bayyana damuwarsu da kuma sanar da cewa sun janye daga duk wata hulɗa da gwamnatin jihar, har sai an ba su kulawar da ta dace.
- Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200
- NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a?
Shugaban mawaƙan jihar, Lawan Gujungu Mai Babban Gandu ne, ya jagoranci taron, inda ya shaida wa manema labarai cewa tun bayan da sabon gwamnan ya hau mulki sama shekara biyu, har yanzu ba su sharɓi romon dimokuraɗiyya ba.
Ya ce mawaƙan sun yi haƙuri na tsawon lokaci suna sa ran za a saka musu, amma abin ya gagara.
A cewarsa: “Mun shiga mawuyacin hali. Muna cikin APC tun asali, mun yi wa jam’iyya hidima sosai a lokacin yaƙin neman zaɓe, mun ƙirƙiri waƙoƙi da dama don tallata manufofin jam’iyyar da kwatanta cancantar ’yan takararta.
“Amma yanzu da muka ci zaɓe kuma muka kafa gwamnati, an watsar da mu tamkar ba mu da wata ƙima.”
Lawan, ya ƙara da cewa daga yanzu mawaƙan za su nisanci duk wani taro ko aikin da ya shafi gwamnati, har sai an saurare su tare da mutunta su da irin gudunmawar da suka bayar.
Wannan bore ya fito fili ne a daidai lokacin da ake buƙatar jituwa da haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar da kuma gwamnatin jihar domin ci gaban al’umma.
Wasu daga cikin mawaƙan da suka halarci taron sun bayyana cewa suna fatan gwamnan zai ji ƙorafinsu kuma ya ɗauki matakin da ya dace, domin ci gaba da gina jam’iyya da gwamnatin da kowa ke alfahari da ita.
Tuni dai wannan batu ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar APC a Jihar Jigawa, inda wasu ke ganin cewa ya kamata gwamnati ta sake duba rawar da waɗanda suka ba da gudunmawa kafin kafa gwamnati, domin gudun fuskantar tawaye.