Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce yana sane da yadda ‘yan Najeriya ke cikin mawuyacin hali sakamakon cire tallafin man fetur.
Shugaban, ya ce ya yi fatan akwai wasu hanyoyin da za a bi don dawo da tattalin arzikin kasar nan ba tare da cire tallafin man fetur ba, amma babu.
- Za mu kara mafi karancin albashin ma’aikata — Tinubu
- An karrama Hajiyar da ta tsinci kudi a Saudiyya
Tinubu, wanda ya bayyana hakan a yayin wani jawabi da ya yi a fadin kasar a ranar Litinin, ya ce ba ya yi hakan ba ne da nufin cutar da talakawa ba.
Ya ce, “Tattalin arzikinmu yana cikin tsaka mai wuya, kuma hakan yana cutar da ku. Farashin man fetur ya tashi. Abinci da sauran farashin kayayyaki sun tashi. Abubuwa da yawa na faruwa sakamakon rashin tabbas.
“Na fahimci wahalar da kuke sha. Ina fata akwai wasu hanyoyi. Amma babu. Idan da akwai, da na bi wadannan hanyoyin kamar yadda na zo nan don taimakawa ba cutar da mutane da al’ummar da nake kauna ba.
“Abin da zan iya bayarwa nan take shi ne na rage nauyi da yanayin tattalin arzikin da muke ciki, musamman kan ’yan kasuwa, ma’aikata da masu raunin cikinmu.
“Tuni, Gwamnatin Tarayya tana aiki kafada da kafada da jihohi da kananan hukumomi don aiwatar da ayyukan da za su rage radadin da mutane ke ciki.”
Shugaban, ya ce ya rattaba hannu kan wasu Dokokin Zartarwa guda hudu a farkon wannan watan bisa ga alkawarin da ya yi na magance manufofin kasafin kudi da kuma yawan harajin da ke dakile yanayin kasuwanci.
Ya yi nuni da cewa, umarnin zartarwa na dakatar da wasu harajin zai samar da abubuwan da suka dace ga masu sana’o’i don habaka kasuwancinsu.