Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya isa birnin Rome na Ƙasar Italiya domin halartar bikin rantsar da sabon Fafaroma, Leo na XIV.
Za a gudanar da bikin ne a wajen wani taron addu’a da ake kira “solemn mass” a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu.
- Crystal Palace ta lashe kofin FA na farko a tarihinta
- Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — Kwankwaso
An tarbi Shugaba Tinubu a filin jirgin sojin Mario De Bernardo, inda jakadiyar Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da jami’an diflomasiyya daga Vatican da ofishin jakadancin Najeriya suka tarbe shi.
Tinubu ya samu gayyata ta musamman daga Sakatare Janar na Vatican, Cardinal Pietro Parolin.
A cikin wasiƙar gayyatar, Fafaroma Leo XIV ya bayyana cewa ya ga dacewar Shugaba Tinubu ya halarci bikin rantsar da shi.
Fafaaroma ya ƙara da cewa Najeriya tana da muhimmanci a gare shi domin ya taɓa aiki a ofishin jakadancin Vatican da ke Legas a shekarun 1980.
Shugaba Tinubu na tare da wasu manyan shugabannin cocin Katolika daga Najeriya ciki har da Archbishop Lucius Ugorji na Owerri, Archbishop Ignatius Kaigama na Abuja, Archbishop Alfred Martins na Legas, da Bishop Mathew Hassan Kukah daga Sakkwato.
Sun tafi Rome ne, domin nuna goyon baya da wakiltar Najeriya a bikin rantsar da sabon Fafaroma.