Sama da mutane miliyan 10.5 a yankin Sahel da ke nahiyar Afirka na iya fuskantar barazanar yunwa a watanni masu zuwa, kamar yadda kungiyar agaji ta Red Cross ta yi gargadi.
Wani abin da ake kira koren yunwa, lokacin da aka yi amfani da wuraren ajiyar abinci a lokacin hunturu da bazara, amma girbi na gaba bai cika ba tukuna, yana kara ta’azzara ta tashe-tashen hankula.
- Shugaban Kasar Nijar ya haramta wa ministoci karin aure
- ‘Yan bindiga sun kashe Sojoji biyu, sun kone Kotu a Anambra
“A wasu wurare a Burkina Faso, mutane suna jiran awa 72 a kan layi don dibar ruwa a rijiyoyin burtsatse.
“Idan lamarin ya kara tabarbarewa, muna iya fuskantar matsananciyar yunwa a tsakanin mutane da dabbobi,” in ji Daraktan ICRC na Afirka, Patrick Youssef.
Akalla mutum miliyan biyu ne ke gudun hijira a kasashen Yammacin Afirka da suka hada da Mali, Burkina Faso, Nijar da kuma Mauritania.
Lamarin ya fi kamari a Burkina Faso, inda mutum miliyan 1.8, wato kashi 10 cikin 100 na al’ummar kasar, aka tilasta wa barin gidajensu.
Burkina Faso dai na fuskantar hare-haren ta’addanci na masu ikirarin kishin Islama.
Kungiyoyin jin kai sun sha kokawa kan rashin samun tallafi ga mutanen da suka fi tsananin bukata.
Yankin Sahel gaba daya yana fama da matsalar sauyin yanayi, inda daya daga cikin fari mafi muni a cikin shekaru da dama da suka gabata ya lalata amfanin gona.