’Yan sanda sun tabbatar da rasuwar mutum 16 a rikicikin sarauta tsakanin kabilun Karimjo da Wurkum a Karamar Hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba.
Kakakin ’yan sandan jihar ya shaida wa Aminiya a ranar Talata cewa kurar ta lafa, momai ya koma yadda aka saba, duk da rayuka 16 da rikicin ya lakume.
- Ruwa Da Iska Ya Kashe Mace 1 da jikkata Wasu 16 A Gombe
- Mahara sun kashe mata da kananan yara a kauyen Filato
Ya bayyana cewa kwamishinan ’yan sandan jihar ya ziyarci garin na Karim Lamido inda aka samu rikicin domin gane wa idonsa abin da ya faru.
A makon jiya Aminiya ta kawo rahoton yadda rikici ya barke a garin Karim Lamido, hedikwatar karamar hukumar, bayan Gwamna Darius Ishaku ya mika sandar mulki ga sabon basaraken garin daga kabilar Wurkum.
Nadin dan kabilar Wurkum a kan sarautar, wadda mahaifinsa ya shafe sama da shekara 40 a kai bai yi wa ‘yan kabilar Karimjo dadi ba.
A kan haka ne bayan dawowar sabon basaraken daga bikin ba shi sandar mulki ‘yan karimjo, da ke ganin su ne ‘yan asalin garin kuma suk neman a nada musu basarakensu, suka tayar da bore.
Rikicin dai ya kai ga kona gidaje sama da guda 100 da lalata gonaki a yayin da ‘yan sanda suka tabbatar da rasuwar mutum 16.
Mutane da dama sun yi kaura sakamakon rikicin zuwa yankunan Lau da Jalingo da Jen da kuma Bambur kafin rikicin ya lafa.