✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mata da kananan yara a kauyen Filato

Gwamna Lalong ya ce maharan sun kai harin ne kafin wayewar garin Talata a yayin da mutanen kauyen ke tsaka da barci.

Ana fargabar an kashe kananan yara da mata da yawa a wani hari da aka kai a kauyen Kubat na Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.

Gwamnan jihar, Simon Bako Lalong, ya tabbatar cewa maharan sun kai harin ne kafin wayewar garin Talata a yayin da mutanen kauyen ke tsaka da barci.

Lalong ya yi Allah-wadai da harin, sannan ya umarci jami’an tsaro da su farauto mahran domin su fuskanci hukunci.

Sanarwar da daraktan yada labaran gwamnan, Makut Simon, ya fitar ta ce Lalong ya umarci hukumomin agaci da na zaman lafiya na jihar su ziyarci kuayen domin gano tantance girmar barnar  da aka yi domin samar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.