Mutum sama da 1,031 ne alkaluma suka tabbatar ’yan bindiga da sauran miyagu sun kashe a cikin watan Yuni a fadin Najeriya.
Bincike ya gano abun ya fi tsanani a Jihar Zamfara inda ’yan bindiga suka kashe akalla mutum 275, sai Jihar Kebbi inda aka kashe mutum 93.
Jihar Neja ita ce ta uku wajen kashe-kashen, inda a watan na Yunin aka kashe mutum 91 baya ga wadanda aka yi garkuwa da su.
Rahoton, wanda wani kamfanin bincike kan tsaro da ke Abuja, Beacon Consulting, ya gudanar ya ce an yi garkuwa da mutane sau 205 a jihohi 34, inda ’yan bindiga suka sace mutum 390 a cikin wata dayan.
Rahoton wanda ya mayar da hankali kan matsalolin tsaro a sassan Najeriya a watan Yuni, ya fi karkata ne a kan hare-haren ’yan bindiga, rikice-rikice, da wasu miyagun laifuka.
Ya kuma gano cewa a Jihohin Bauchi da Gombe ne kadai ba a samu rahoton kashe-kashe ko satar mutune ba a cikin watan Yuni.
Sai dai ya ce ’yan bindiga su ne matsalar tsaron da fi ci tsanani a cikin matsalolin tsaron da ya gano a kananan hukumomi 127 a Najeriya.
Amma duk da haka, kungiyar Boko Haram da kawayenta sun kashe kashe mutum tara suka kuma sace wasu 20 a watan da ya gabata.
Sai kungiyar IPOB da ta kashe mutum 18 a hare-hare 12 da ta kai a cikin watan mai kwana 30.
– Matsalar a yankunan Najeriya –
Matsalar ta fi muni a yankin Arewa maso Yamma inda aka kashe mutum 416 aka kuma yi garkuwa da wasu 280 a kananan hukumomi 28.
A Arewa ta tsakiya, an kashe mutum 218 an sace was 24, sai Arewa maso Gabas inda aka kashe mutum 188 aka kuma sace wasu 22.
A yankin Kudu maso Gabas an kashe mutum 117 an yi garkuwa da 26; Kudu maso Yamma an kashe 74 an sace 27; Kudu maso Kudu kuma aka kashe 18 aka sace 11.
– Arewa ta Yamma –
A Arewa maso Yamma, inda matsalar ta fi kamari, rahoton ya ce ’yan bindiga sun kashe mutum 275 a Zamfara, amma ba su yi garkuwa da ko mutum daya ba a Jihar, wadda hare-haren bata-garin suka jefa akasarin mazauna karkara cikin fatara ko tilasta musu yin kaura.
Sai makwabciyarta Jihar Kebbi, inda aka sace mutum 119 baya ga 93 da aka kashe.
Jihar Kaduna ita ce ta uku inda aka kashe mutum 26, aka yi garkuwa da wasu mutum 157.
A Jihar Katsina, an kashe mutum shida an sace wasu uku; Sakkwato an sace mutum 15 amma babu kisa; sai Kano da Jigawa inda aka kashe mutum dai-dai, amma babu garkuwa da mutane.
– Arewa ta Tsakiya –
Jihar Neja ce kan gaba a yankin Arewa ta tsakiya — an kashe mutum 91 an sace uku.
A Binuwai an kashe mutum 72 an sace daya; sai Jihar Filato a matsayi na uku, inda aka samu kashe-kashe 27 da kuma sace mutum daya.
A Kwara an kashe mutum 11 amma babu garkuwa; Kogi da Abuja kuma a kowannensu an kashe mutum uku an sace wasu 10.
Rahoton ya ce ’yan bindiga sun fi addabar yankunan Arewa maso Yamma da Kuma Arewa ta Tsakiya duk kuwa da kokarin hukumomin tsaro na fatattakar su.
“A tsawon lokacin, an yawaita kai munanan hare-hare a kauyukan jihohin Kaduna, Katsina, Neja, Sakkwato, da Zamfara tare da sace dimbin dalibai a makarantu a Jihohin Kebbi, Kaduna da Neja, baya ga iyalan ma’aikatan makarantu da kuma marasa lafiya da jami’an lafiya a wata cibiyar kula da lafiya a Jihar Kaduna.
“Akwai kuma inda ’yan bindiga suka kafa shingen bincike har suka yi garkuwa da matafiya suka kuma kashe wasu a kan hanyar Kaduna zuwa Kachia.
“Mun kuma lura da kawancen da aka kulla tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin Arewa maso Gabas da yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya,” a cewar rahoton.
– Arewa maso Gabas –
Mutum 101 ne rahoton ya ce an kashe a Arewa maso Gabas, a kananan hukumomi takwas a Jihohin Borno, Yobe, Adamawa da Taraba.
Daga ciki akwai harin Boko Haram a wani kauye, inda kungiyar ta kashe dan sanda, ta kona kayan Majalisar Dinkin Duniya a Jihar Yobe.
An kuma kashe mayakan ISWAP sama da 50 a Borno, da kuma wasu shida a yankin Dikwa a Jihar.
A Adamawa kuma ’yan bindiga sun kai hari kauyen Gadawaluwol inda suka kashe mutum daya.
Sai makiyaya da suka kashe wani magidanci da ’ya’yansa biyu a kauyen Galang Jauro a Jihar Taraba.
– Kudu maso Gabas –
A Kudu maso Gabas mutum 117 aka kahse, aka sace 26 a kananan hukumomi 20 a jihohin Enugu, Anambra, Abia da Ebonyi.
Abubuwan da suka faru a yankin sun hada da harin bom, harin jirgin sama, harin ’yan bindiga, rikicin masu dauke da makami, da rikici tsakanin al’ummomi.
– Kudu maso Kudu –
Mutum 17 aka kashe a Kudu maso Kudu, aka sace mutum daya a kananan hukumomi 15 na jihhin Edo, Ribas, Delta, Kurso Riba, da kuma Akwa Ibom.
Matsalolin da aka samu a yankin na Kudu maso Kudu su ne harin bom, harin jirgin sama, harin ’yan bindiga, rikicin masu dauke da makami, da rikicin al’ummomi.
– Kudu maso Yamma –
A Kudu maso Yamma kuma an kashe mutum 74 tare da yin garkuwa da wasu 27 a kananan hukumomi 30 a jihohin Oyo, Osun, Ekiti, Ondo, Ogun, da Legas.
Mastalar tsaron da aka samu a yankin a cikin watan na Yuni sun hada da harin bom, harin jirgin sama, harin ’yan bindiga, rikicin masu dauke da makamai, da rikici tsakanin al’ummomi.
Daga Sagir Kano Saleh, Fidelis Mac-Leva da Idow Isamotu