✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 10 sun shiga hannu kan zargin aikata laifuka a Bauchi

Rundunar ta ce za ta gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutum 10 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.

An kama wadanda ake zargin ne da laifin fashi, garkuwa da mutane, hada baki, cin zarafi da sauransu.

Sanarwar da kakakin rundunar, SP Ahmed Wakil ya fitar ranar Talata ta ce, “Jami’an da ke aiki da bataliyar SF ta 133 da ke Azare a Karamar Hukumar Katagum ne suka mika wa rundunar ’yan sanda wadanda ake zargi,” in ji shi.

Wakil, ya ce wadanda ake zargin sun yi garkuwa da wani Ojo Tobi David, dalibi a ajin karshe na Jami’ar Tarayya da ke Gadau a Bauchi.

Ya ce wadanda ake zargin sun kuma kwace wata mota kirar Toyota Camry mai lamba: KYW 925 SB bayan sun yi garkuwa da mai motar a kan hanyar Misau zuwa Azare.

“Amma daya daga cikin wadanda ake zargin da ke unguwar Turum a Bauchi, ya shiga hannun lokacin da yake kokarin tserewa.

“An kai shi Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Azare domin a kula da shi cikin gaggawa amma likita ya tabbatar da mutuwarsa.

“Lokacin da aka samu bayanan, sojojin da ke a shingen binciken ababen hawa na Azare zuwa Misau sun kai dauki nan take sannan suka tare motar da suka sace.

“An ceto wanda aka sace ba tare da ya ji rauni ba,” in ji shi.

Ya ce binciken farko ya nuna cewar wadanda ake zargin sun samu rashin fahimta kan raba kudi Dala 3,800 da suka samu ta hanyar zamba.

Ya ce za a mayar da su zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike.