Gwamnatin sojin Nijar ta ce tana tsara matakan da kowane bangare zai amince da shi game ficewar sojojin Faransa daga kasar.
Sanarwar da gwamnatin ta fitar kafin wayer garin Talata ta ce jazaman ne a cimma dadaito tsakaninta da Faransa kan “hakikanin lokacin” da sojojin na Faransa za su gama ficewa daga Nijar.
- Wata 2 babu Bazoum: Halin da Nijar ke ciki bayan juyin mulki
- Kofin Afirka: Wace kasa za ta karbi bakuncin gasar 2025
Sanarwa na zuwa ne wata biyu cur bayan sojojin sun kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, wanda suke ci gaba da tsarewa kan zargin cin amanar kasa.
Tun da farko sun nemi sojojin Faransa, babbar kawar Gwamnatin Bazoum su bar kasar amma gwamnatin Faransa ta ki, bisa hujjar cewa Bazoum ne halastaccen shugaba kuma da gwamnatinsa ta kulla yarjejeniyar tsaro a Nijar.
Bayan wata biyu ana kai ruwa rana, har da tsare jakadan Faransa ofishinsa da ke birnin Yamai, Shugaba Emmanuel Macron ya sanar a ranar Lahadi cewa jakadan da sauran ma’aikatan ofishin jakadancin suna hanyarsu ta dawowa birnin Paris.
A lokacin ne Mista Macron ya sanar cewa nan da ’yan makonni Faransa za a dakatar da aikin sojinta na samar da tsaro a Nijar, inda za ta gama kwashe sojojinta daga kasar zuwa karshen shekarar da muke ciki.
Ya ce duk da cewa masu juyin mulkin na Nijar sun hana jiragen kasarsa shawagi a sararin samaniyar kasarsu, gwamnatin Faransa za ta tattauna da su domin tsara yadda ficewar sojojinsa zai kasance daga Nijar.
Tuni dai sojojin Nijar suka yi maraba da hakan.