✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kofin Afirka: Wace kasa za ta karbi bakuncin gasar 2025

Ana hasashen zawarcin gasar 2025 zai yi zafi tsakanin Morocco da Algeria wadanda ke zaman doya da manja

A ranar Laraba za a sanar da sunayen kasashen da za su karbi bakuncin Gasar Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka a shekarar 2025 da kuma na 2027.

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar (CAF) ta riga ta sanar cewa Kasar Ivory Coast ce za ta dauki nauyin gasar ta 2024, daga ranar 13 ga Janairu zuwa 11 ga Fabrairu, 2024

Najeriya na zawarcin daukar nauyin gasar 2025 da hadin gwiwar Jamhuriyar Benin; Haka ma kasar Zambia da Morocco da Ajeriya ke cikin masu neman damar zama masu masaukin baki.

Sai dai wasu hasashe dai na ganin kasashen Morocco ce za ta samu damar daukar nauyin gasar a 2025, sai kuma Algeria a 2027 a yayin bikin da zai gudana a birnin Alkahira na kasar Masar a ranar Laraba.

A yayin da kowanne daga Morocco da Algeria ke neman daukar nauyin gasar ta 2025, Algeria na cikin masu zawarcin gasar 2027.

Haka su ma kasashen Masar, Senegal da Botswana, a yayin da Kenya-Tanzania-Uganda suka yi hadin gwiwa.

An dade ana sanya lokaci ba tare da bayyana wadanda sunan mai masaukin bakin gasar ba, ammwa kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce, “tabbas a ranar 27 ga Satumba za a sanar da sunan kasashe biyu.”

Mambonin kwamitin gudanarwar gasar za su kada kuri’a bayan tantance duk kasashen da ke takarar karbar bakuncin gasannin na 2025 da kuma 2027.

Sai dai kuma sha’anin siyasa da kuma tsarin karba-karbar bakuncin gasar a nahiyar sun kara haifar da sarkakiya.

Kasashen Algeria da Morocco makwabtan juna ne a yankin Arewacin Afirka, amma ba sa ga-maciji da juna, har a harkar kwallon kafa a wannan shekara.

Haramta wa jiragen Morocco shawagi a sararin samaniyar Algeria, wadda ta karbi bakuncin a 2022/2023 ya hana tawagar ’yan wasan Morocco na cikin gida halartar Gasar Kofin Nahiyar Afirka (CHAN).

A baya sau biyu Morocco ta lashe gasar, amma hana ’yan wasanta bi ta sararin samaniyar Algeria ya sa ta kaurace wa gasar.

Kasashen biyu dai na takama da katafarun filayen wasa da tarin masoya kwallon kafa, da kuma kwarin gwiwarsu na daukar nauyin gasa da za ta kayatar da duniya.

Kowannensu kuma na son a ce shi ne zai dauki nauyin gasar ta 2025.

Jawabin da wani babban jami’in CAF dan kasar Morocco Fouzi Lekjaa ya yi wa ’yan siyasar kasar cewa kasarsu ce za a zaba ya tayar da kura.

Sharadin karbar bakuncin gasar su hada da wajibi ne kasar ta kasance tana da filayen wasa akalla guda biya da kowanne ke iya daukar mutum 40,000, da wasu hudu masu daukar akalla mutum 20,000.

%d bloggers like this: